A ranar Talata 26 ga Satumba, 2023 Majalisar Dattawa za ta tantance Dakta Olayemi Michael Cardoso, a matsayin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Majalisar za ta kuma tantance mutane hudu da aka mika sunayensu ga majalisar a matsayin mataimakan shugaban Bankin CBN, wadanda kuma za su kasance a matsayin Kwamitin Gudanarwa da tafiyar da harkokin babban bankin har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
- Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Cardoso A Matsayin Sabon Gwamnan CBN
- CBN Ya Kara Kudin Ruwa Mafi Tsada A Cikin Shekara 22
A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na shugaban majalisar dattawa, Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya fitar a yammacin ranar Litinin, majalisar za ta tantance dukkan wadanda aka mika sunayensu ga majalisar bayan ta dawo hutun shekara a ranar Talata.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, a ranar 15 ga watan Satumba ne shugaba Tinubu ya amince da nadin Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin kasa (CBN).
Ya kuma amince da nadin mataimakan gwamnan su hudu na tsawon shekaru biyar kowanne a matakin farko in sun samu amincewar majalisar dattawa.