Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nuni ga ikon da kasashe mambobin kungiyar BRICS ke da shi na kasancewa muhimmin karfi, dake juya akalar harkokin duniya zuwa hanya mai bullewa, yana mai bayyana bukatar kara samar da tabbaci, da daidaito, da karsashi mai kyau ga duniya.
Shugaba Xi, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba 23 ga watan nan, yayin taron jagororin BRICS karo na 15 dake gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, ya kara da cewa, duba da cewa shugabannin kasashe mambobin kungiyar su 5, sun amince da shigar duniya wani yanayi na tangal tangal, da sauye sauye, kungiyar BRICS a daya hannun za ta iya ingiza samar da tabbaci ga duniya, kuma wannan batu ya zamo muhimmi a tattaunawar ta wannan karo.
Xi Jinping ya kuma ce kasashen na BRICS, sun zama muhimmin karfi dake sarrafa akalar al’amuran kasa da kasa. Kuma ko wacce daga cikin su ta zabi hanyarta ta neman ci gaba, tare da hada gwiwa da sauran wajen kare burin ci gaba tare, da aiki tare wajen zamanantarwa, wanda hakan ke alamta alkiblar al’ummun duniya, zai kuma zurfafa yanayin ci gaban duniya baki daya.
Har ila yau, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar BRICS, muhimmin mataki ne na hade zamanin da da na yanzu, da dorawa kan inda aka tsaya. Don haka akwai bukatar dukkanin sassa su rungumi ainihin burin da aka sanya gaba, na dinkewa wuri guda da samun bunkasuwa, da karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, da ingiza kawance mai inganci, da yayata sauye sauye a jagorancin duniya, ta yadda za a yi tafiya kan tafarki na gaskiya kuma mai ma’ana.
Kaza lika a shigar da tabbaci, da daidaito, da karsashi cikin harkokin duniya. Game da hakan, shugaba Xi Jinping ya ba da shawarar aiwatar da hakikanin matakai masu nasaba da samar da ci gaba, da tsaro, da dinke sassan wayewar kai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)