A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym Jomart Tokayev a birnin Xi’an, gabanin su halarci taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na farko. Baya ga halartar taron da za a bude a gobe Alhamis, shugaba Tokayev, zai kuma gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin.
Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya yiwa shugaba Tokayev maraba da halartar taron na koli, da kuma ziyarar aiki da zai gudanar a Sin. Ya ce alakar Sin da Kazakhstan ta shiga wani sabon mataki na cika “Shekaru 30 masu daraja”.
Don haka ya dace sassan biyu su kara azamar yayata kawancen gargajiya dake tsakanin su, su goyi bayan juna, tare da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna.
A dai yau din, shugaba Xi ya saurari rahoton aiki daga gwamnatin lardin Shaanxi, tare da yin na’am da irin manyan nasarorin da aka cimma a fannoni daban daban. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)