“Kasar Sin tana da dimbin fannonin kasuwanci” kuma “Tsarinmu na samar da kayayyaki a kasar Sin yana gudanar da ayyukan kirkire-kirkire da yawa na duniya…”
Wannan furucin ya fito ne daga bakin Xia Xueying, mataimakiyar babbar darektar kamfanin Schneider Electric na kasar Faransa a yayin da take zantawa da wakilin CMG a lokacin bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya wato CISCE karo na uku, da har yanzu ake gudanarwa a birnin Beijing na kasar Sin.
Ta kuma kara da cewa, “Kasar Sin babbar kasuwarmu ce ta biyu a duniya, wadda take da manyan sansanonin samar da kayayyaki, da kasuwanni masu kirkire-kirkire dake bude kofa ga kasashen waje. Gwamnatin kasar Sin ta dade da nacewa kan bude kofa ga kasashen waje, tare da samar da yanayin kasuwanci mai kyau, kana tsarin samar da kayayyaki na kasar na da babban karfin yin takara sakamakon ingancinsa.” (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp