Tsohon babban hafsan hafsoshin Nijeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bayyana cewa an kashe akalla hafsoshi 2,700 da sojoji sama da shekaru 12 a yakin da ake yi da Boko Haram.
Ya kuma musanta raɗe-raɗin da ake yi na cewa, jami’ai da hafsoshin sojoji na wani addini ne akafi turawa fagen yaki, saboda a kashe su.
- Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
- Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya?
Irabor ya bayyana haka ne a cikin sabon littafinsa mai suna “SCARS: Journey Nigeria and the Boko Haram Conundrum,” wanda aka kaddamar kwanakin baya.
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.”
Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.”














