Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa za a cimma yarjejeniya don kawo ƙarshen yaƙin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Gaza da Isra’ila, tare da sakin fursunonin ƙasashen biyu.
Ana sa ran a yau Laraba, za a koma teburin sulhu don ci gaba da tattaunawa kan abubuwan da ke haifar da koma baya ga yarjejeniyar, ƙarƙashin jagorancin Firaministan Qatar da shugaban hukumar tsaro ta CIA.
- Sin Na Maraba Da Abokai Daga Kasashen Waje Da Suka Kara Mayar Da Hankali Da Ziyartar Kasar
- Kano Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Miƙo Mata Rabonta Na Tsawon Shekaru 25 Daga Shirin NLNG
Sai dai ko a ranar Talata, ma Isra’ila ta kai harin sama kan wani gini a Gaza, wanda ya yi ajalin kusan mutum 10 kana baraguzan gini ya danne wasu da dama kamar yadda likitoci suka tabbatar.
Idan ba a manta ba kwanakin baya an sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, wanda har wasu al’umma sun fara kyautata zaton cewa somin zaman lafiya a yankin kenan, kafin daga baya sabbin hare-hare suka ci gaba.