• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata A Sake Yi Wa Tsarin Ɗaukar Kuratan Ƴansanda Garanbawul

byRa'ayinmu
2 months ago
Ƴansanda

Al’umomin a ƙasar nan, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, kan batun kalubalen rashin tsaro da ke ci gaba da addabar ƙasar. Akasari, an fi yin batun kan yunkurin da jami’an sojin kasar ke ci gaba da yi, na dakile matsalar.

Wannan ya yi daidai da irin gudunmawar da sojin ke bayar wa ne, wajen kare kimar kasar daga dukkan wasu hare-hare, musamman duba da cewa, aikin sojin, ba wai kawai, tabbatar da tsaro, a cikin kasar bane, wajen karfafa doka da oda, a cikin kwayar kasar ba.

Sai dai, a ra’ayin wannan Jaridar, mun lura da irin mahimmancin da sojin suke da shi, wajen karafa tasro a cikin kasar, musamman duba irin, tabarwarewar, lamarin tsaro.

Kazalika, wannan kokarin na soji, ba wai kawai, za yi watsi da nauyin da kundin tsarin mulkin kasar, ya dorawa jami’an ƴansanda bane, na gudanar da ayyukan tsaro, a cikin kasar ba.

ɗaukin da soji ke bayar wa wajen tabbatar da tsaro a cikin kasar, ana yi ne, domin kaucewa, take doka da oda, gaba daya.

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

  • Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka
  • Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana

Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin.

ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa,  daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa, ya bayar da umarnin yin hakan, tare da yarjewar, gammaiyyar Majalisun kasar.

Amma a nan, kamar yadda kudin tsarin mulkin kasa ya fayyace, sojin ba su da wani hurumin, maido da  doka da oda, a cikin kwayar kasar.

Sai dai, shugaban kasa na da ikon umartar shigo da soji kan batun dawo da doka oda, domin su taimaka wa ƴansanda.

Wannan kiran na a yiwa tsarin ɗaukar kuratan ƴansandan, za a iya cewa, tsohon batu ne, kusan tun a Jamhuriyya ta hudu ta kasar nan.

Ko da yake dai, wasu gwamnatocin baya, sun yi yunkurin yiwa tsarin garanbawul, sai dai, ba a yi, wani abin azo a gani, kan batun ba.

Misali, tsohowar gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a 2006, ta kafa wani kwamati na Fadar shugaban kasa, da ɗan Mandami ya jagoranta, domin a samar da sauye-sauye, a aikin ƴansanda.

Bugu da kari, a lokacin mulkin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Yar’Adua a 2008, ya kafa kwamtin Fadar shugaban kasa, karkashin shugabancin Muhammadu ɗikko Yusuf.

Kazalika, a 2012 tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamtin Fadar shugaban kasa, a karkashin shugabanci Parry Osayande.

A 2018 an kafa kwamitin Fadar shugaban kasa na samar da sauyi kan batun dakarun ƴansanda da ke yakar masu yin fashi da makami wato SARS.

Sai dai, duk irin wannan kokarin da aka yi a baya, matsalar ba sake Zane ba

A nan muna nuna damuwarmu, kan rashin samar da tsarin da ya dace, na yin sauye-sauye a aikin na ƴasanda.

Ra’ayin wannan Jaridar, ya zo daidai da cewa, batu daya da ke kawo cikas kan samar da ingantaccen tsari a aikin na ƴansanda shi ne, na rashin kyakyawan ɗaukar jami’an aikin.

ɗukkan irin sauye-sauyen da za a samar na ɗaukar kuratan, zai yi wuya a cimma wata nasarar kirki, matukar tsarin na ɗaukar kuratan, ya ci gaba da zama, ana yinsa, ba bisa ka’ida ba.

Batun ɗaukar kuratan ba abu ne na was aba, dole ne rinka ɗaukar kuratan, masu halayya ta gari ba masu kashi a gindi ba.

Idan za a iya tunawa, a 2024, an tayar da Jijiyar Wuya a tsakanin rundunar ƴansanda ta kasa da Hukumar kula da aikin ƴan sanda na kasa, kan batun ɗaukar kurata sama oɓer 10,000 da kuma ɗaukar, kurata na musamman.

An ruwaito Kakakin runudanar ƴansanda na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi, ya shelanta cewa, ɗaukar wadanan kuratan na cike da kura-kurai da dama da aka tabka, ciki har da na zargin cin hanci, har da kuma sanya sunayen wasu, da ma ba su nemi shiga aikin ba, wasun kuma, ba su iya tsallake gwaje-gwajen da aka yi masu na kiwon lafiyarsu ba.

Hakazalika, a 2022 a lokacin mulkin toshon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, gwamnatinsa ta kirkiro da sabon tsari ga aikin, musamman domin a tabbatar da an inganta aiki yadda zai iya yakar duk wani nau’I, na aikata manyan laifuka da kare rayukan yan Nijeriya da kuma dukiyoyinsu a karkashin doka ta  2020.

Sai dai, duk da hakan, wannan manufar, hakar bata cimma ruwa ba, musamman kan batun ɗaukar ingantattun kuratan.

Kazalika, a kwanan baya, Ma’aikatar Kula da Jindadi da Walwalar ƴansanda tare da hadaka da rundunar ƴansanda ta kasa, ta kaddamar da  kudurin farfado da aikin ƴansanda.

Sai dai, Ma’aikatar a cikin wannan kudirin, ba ta tabo batun tsarin yin garanbawul kan ɗaukar kuratan ba.

Ko da yake dai, wannan Jaridar ta jinjinawa wannan kokarin na mahukuntan ƴansandan da suka yi a baya, amma Jaridar, na da ra;ayin cewa, dole ne a samar da kyakyawan tsari na ɗaukar kuratan ƴansandan, musamman a tabbatar da ba dauki wadanda ke wani guntun kashi, na aikata laifi ba. Yin hakan shi ne, babban ginshiki kuma madogararmu, a nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Next Post
Taɓarɓarewar Tarbiyyar Matasa A Arewa: Ƙalubalen Da Ke Gaban Iyaye Da Shugabanni

Taɓarɓarewar Tarbiyyar Matasa A Arewa: Ƙalubalen Da Ke Gaban Iyaye Da Shugabanni

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version