Ya zuwa ranar Laraba, adadin wadanda suka rasa rayukansu a yankunan kasar Syria dake karkashin mulkin gwamnatin kasar, sakamakon mummunar girgizar kasa 2 da ta aukawa wani yankin kasar Türkiye dake dab da Syrian, ya kai mutum 1250, yayin da wasu 2054 suka jikkata.
Sai dai a cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria, takunkumin da kasar Amurka da kawayenta na yammacin duniya suka sanya wa kasar, ya sa ana fuskantar karancin na’urori masu taimakawa aikin ceto. Lamarin da ya dakile aikin ceton mutanen da baraguzan gine-gine suka binne su.
Ganin haka ya sa kungiyoyi daban daban, irinsu Syrian Arab Red Crescent, da kwamitin yakar ra’ayin nuna bambanci na kasashen Larabawa da Amurka, yin kira ga kasar Amurka da kawayenta, da su soke takunkumin da suka sanya wa kasar Syria cikin sauri, ta yadda za a iya magance lalacewar yanayin jin kai a kasar. To sai dai kuma duk haka, kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Ned Price, ya ce kasarsa ba za ta tuntubi gwamnatin kasar Syria, dake karkashin jagorancin shugaban kasar Bashar al-Assad ba.
A kwanakin nan, dimbin kasashe da yankuna, ciki har da kasar Sin, sun samar da agaji ga kasashen Türkiye da Syria ba tare da wani jinkiri ba, abin da ya nuna yadda kasashe daban daban suke kokarin yin hadin gwiwa don tinkarar bala’i daga Indallahi. Sai dai abun da kasar Amurka ta yi ya sha bamban da na sauran kasashe.
Don haka dai ya kamata ‘yan siyasan kasar Amurka, wadanda suka saba da ambatar “hakkin dan Adam”, su dauki hakikanin mataki, don taimakawa mutanen kasar Syria da suke shan wahalar Iftila’i. (Bello Wang)