Bayan da kasar Sin ta kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, wasu kasashe sun sanar da matakan yiwa Sinawa dake da niyyar shiga kasashen gwajin cutar, ko da yake akwai wasu kasashe da dama dake bayyana cewa, ba za su sauya tsarinsu domin yiwa Sinawa dake son shiga kasashen gwaji ba.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata kasa da kasa su dauki matakai masu dacewa, da nuna ra’ayi iri daya ga dukkan jama’ar kasashen duniya, kuma bai kamata a haifar da illa ga mu’amala, da hadin gwiwa a tsakanin jama’ar kasashen duniya ba.
Wang Wenbin ya ce, cikin shekaru 3 da suka gabata, kasar Sin ta rika sauya matakan da take aiwatarwa na kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 bisa halin da ake ciki, amma duk da sauye-sauyen da aka samu, manufar kasar ta fifita kare al’umma, da tsaron rayukansu ba ta sauya ba.
Wang ya kara da cewa, wasu kafafen watsa labarai na yammacin duniya na ta cewa, wai sauyin matakan da Sin ta fara aiwatarwa a baya-bayan nan na nuna sauyin manufa ne, kuma hakan na nufin gwamnatin Sin ta canza matsaya, game da muhimmancin da take dorawa wajen mayar da jama’a gaban komai. Wang Wenbin ya nuna cewa, irin wannan zargi ya sabawa gaskiya, da shaidu na kimiyya, kuma ana furta su ne kawai da wata mummunar manufa.
Kaza lika, Wang Wenbin ya ce tun bayan barkewar annobar, Sin ta ci gaba da mayar da aikin kare rayukan jama’a gaban komai, ta kuma yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da lafiyar al’umma, kana an yi duk abun da ya dace, don samar da jinya ga masu bukata. Har ila yau, cikin matakan yaki da wannan annoba, Sin ta ci gaba da tsara matakai daban daban, na kandagarki da shawo kan cutar tare da sauran muhimman ayyukan raya tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma yadda ya kamata. Bugu da kari, gwamnatin kasar ta ci gaba da daidaitawa, da kyautata matakan kandagarki da shawo kan cutar bisa yanayin da ake ciki. (Masu Fassarawa: Zainab Zhang, Saminu Alhassan)