Kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da zaben gwamna Biodun Oyebanji na Jihar Ekiti da mataimakiyarsa Misis Monisade Afuye.
Kotun da ta yanke hukunci ranar Alhamis a Ado -Ekiti ta yi watsi da karar dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Mista Segun Oni.
- Ya Kamata Kasa Da Kasa Su Dauki Matakai Iri Daya Na Magance Yaduwar Cutar COVID-19 Ga Dukkan Jama’ar Kasashen Duniya
- PDP Ta Yi Barazanar Hukunta Gwamnonin G-5 Kan Hada Kai Da Tinubu
A hukuncin da alkalin kotun, Mai Shari’a Wilfred Kpochi da mamba a kwamitin, Mai Shari’a Sa’ad Zadawa suka karanta, sun warware duk wasu batutuwan da suka shafi Oni da jam’iyyarsa ta SDP.
Talla
Kwamitin ya ce karar da Oni ya shigar kan Oyebanji da Afuye, “ya gaza samar da cikakkiyar hujja.”
Talla