ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Kasashen Turai Su Kara Fahimtar Kasar Sin Don Karfafa Dangantakar Dake Tsakaninsu

by CGTN Hausa
2 years ago
Turai

A jiya Alhamis ne, aka kaddamar da taron shugabannin kasashen Sin da EU karo na 24 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin ganawarsa da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel da shugabar kungiyar tarayyar kasashen Turai Ursula von der Leyen, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su tsaya tsayin daka, kan raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, da kara fahimtar juna, domin inganta dangantakar dake tsakaninsu da zuciya daya.

A nasu bangare, shugabannin kasashen Turai sun ce, ba su son neman raba-gari da kasar Sin, kuma sun yi imanin cewa, bunkasuwar kasar Sin cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba ta dace da moriyar kasashen Turai.

  • Fu Qiaomei: Matashiyar Masaniyar Kimiyyar Kasar Sin Da Ta Sake Rubuta Tarihin Dan Adam Na Da
  • Shugabancin JKS Ya Gudanar Da Taro Game Da Ayyukan Raya Tattalin Arzikin Kasa Na 2024

A cewar wasu manazarta, Sin da EU sun aike da wani sako mai kyau don tinkarar kalubale ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa, wanda ya dace a yi maraba da shi.

ADVERTISEMENT

A bana ake cika shekaru 20 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da EU, yadda bangarorin biyu suka raya dangantakar dake tsakaninsu cikin shekaru 20 da suka gabata, ya nuna cewa, idan aka dauki juna a matsayin abokai, aka kuma martaba juna, to, tabbas, huldar dake tsakaninsu za ta kara bunkasa. A cikin shekaru 20 masu zuwa, akwai bukatar bangarorin biyu su kara fahimtar juna, da daga huldar dake tsakanin Sin da Turai zuwa wani sabon matsayi, a lokacin da suke dukufa wajen inganta zamanintarwar kasar Sin da dunkulewar kasashen Turai tare. Hakan ba wai kawai zai amfanar da jama’ar bangarorin biyu ba, har ma zai kawo karin kwanciyar hankali da tabbaci ga duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Gwamna Yusuf

Gwamnan Kano Zai Gana Da Shugaban ‘Yan Fansho Kan Batan Naira Biliyan 5

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.