A kwanakin baya, shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen, ta sanar da sakamakon bincike kan batun hana motoci masu amfani da wutar lantarki da Sin ta kera samun rangwame daga gwamnati.
Game da wannan batu, kasashen Turai sun tattauna sosai. Wasu dake da cikakken sanin ya kamata na kasashen Turai na nuna cewa, shawarar da EU ta yanka ta bayyana tsoron yin takara cikin adalci, da daidaito na wasu kasashen Turai.
A cikin wadannan shekaru da suka gabata, motoci masu amfani da wutar lantarki na bayyana karfin takara mai inganci, kuma muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne, kamfanonin Sin sun mai da hankali kan wannan batu tun da wuri, sun kuma kara karfin kirkire-kirkire, tana da cikakken tsarin samar da irin wadannan motoci fiye da saura. Sabanin hakan, kasashen Turai sun dade suna mai da hankali kan motoci masu amfani da mai, duk da cewa sun yi jinkiri a kwaskwarimar da suke yi don karkata zuwa hakan. Hakan ya sa, wasu kasashen Turai, da manyan kamfanonin motoci ke damuwa, cewa motocin da Sin ta kera za su mamaye kasuwannin su. Wannan shi ne dalilin da ya sa EU ta fara bincike kan batu. (Amina Xu)