Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum.
A gun taron, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna rashin gamsuwa ga wasu kasashen da suka yi batanci a kan aikin ‘yan sandan yankin Hong Kong. Inda ta yi kiran cewa, ya kamata kasashen da abin ya shafa su mutunta ikon mulkin kasar Sin da tsarin dokoki na Hong Kong, su daina ba da goyon baya ga masu adawa da Sin wadanda ke tayar da tarzoma a Hong Kong.
Game da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin sanyi ta yankin Asiya karo na 9 da birnin Harbin na Sin zai karbi bakunci a shekarar 2025 kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa, wannan wata babbar gasar wasanni ce ta kasa da kasa wacce kasar Sin ta gudanar bayan gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, kuma wata dama ce ga Sinawa da al’ummun kasashen waje su zurfafa mu’amala da karfafa abokantaka a tsakaninsu. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp