Duk sanda akace mutum yana da dan abun juyawa duk kankantar sa tabbas ya karawa kansa kima sannan ya ragewa kansa damuwa.Mace mau sana’a ko a wurin dangin miji kimarta daban take balle kuma akai ga shi kanshi mijin.To idan kuma uwargida ta maida kanta sai anci an bata to fa tabbas ta hadu da aikin jira dan kuwa duk yanda kike so kiyiwa kanki abu dole ki hakura sai an dauko an baki.
Kamar yadda aka sani uwargidan da batada kwakwarar sana’a adinga inda kaganta zaka tafita daban acikin tsara,kuma rashin dan na kashewa yana janyo abubuwa da Dama musamman a zamantakewar aure.
- Kullum Tirela 200 Ce Za Su Riƙa Ɗaukar Mai A Matatar Fatakwal – Fadar Shugaban Ƙasa
- Sin Ta Yi Tir Da Matakin Amurka Na Sayarwa Taiwan Makamai
Abu na farko mace mara sana’a zata kasance kullum cikin kunci bata san me ke mata dadi ba musamman ma idan mijin ba mai hali ba ne sosai,zata kasance ko zamantakewar ta da miji ma babu dadi kawai sai taji tana jin haushin shi batare da yayi mata wani kwakwaran laifi ba .
Rashin sana’a na sa uwar gida ko acikin danginta ta zama mujiya ta koma kamar bare,sai abinda akaci aka bata ,ko shawara za ayi sai taga ana damawa kannenta masu dan abun hannun su amma ita kuwa ta zama bare.
Hakazalika rashin abin yi na sa uwargida ta zama ‘Depressed’ wato ta kasance cikin kuci ba tada walwala. Amma yau in uwargida zata samu dan abin juyawa zata kasance batada lokaci zama tayi tunanin banza ba lokacin ta zai kasance na juya taro ya koma sisi ne.
Kamar yadda mawakiya Barmani Choge ta ke kirari a wakarta inda take cewa ‘a kama sana’a mata zaman banza ba namu ba’ to wannan magana haka take .Uwargida in kika kama sana’a ke kanki zakiji kin fi samun natsuwa yan kananan hidimar ki ba sai kin jira miji ya zo ya miki ba.Haka yara zaki taimakawa maigida da dan kanana hidimansu wanda dai baifi karfin ki ba, kuma ko su kansu yaran sun san ana musu in suna da dan bukatun su zakiga sun nufo ki amma ba wai in sunzo sun ce a basu kusin fensir ba ki ce to ku jira Baban ku ya dawo .Wannan yana rage daraja har a idon maigida.
Uwagidan da ta rike sana’a ko shi kanshi mijin yanda zai mata magana cikin fahimta daban ne da wacce take zaune zai an daga sai an tayar. In uwargida na juya biyar ta koma goma za taga yanayin zaman lafiya a gidan ma ya karu babu yawan gaba,babu yawan jin haushin juna ko kuma hantara.
Sana’a nasa miji ya kalle mace da daraja sa kuma kima saboda yawan bani bani ko a gidan ku ne yana jawo raini amma in kika kasance kina dan daukewa maigida wasu nauyi to fa duk duniya babu kamar ki.
Koda ace uwar gida tana hidima mijin baya nuna halin ko in kula yanuna kamar bai sani ba to fa cikin ransa ba karamin farin cikin yake yi ba dan yasan dole akwai kina dauke masa wasu tallafi.
Mata a gyara a rage zaman banza, a nemi sana’a akwai sana’o’i iri daban daban kala kala sai wanda kika zaba kamar su Dinki,turaren wuta, saida itace,saka,da dai sauran su kuma duk wanda uwar gida tasa kai zata iya kuma zata samu alheri sosai dan ta tallafawa kanta har ma da ‘yan uwanta.