Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ya zama wajibi kasashen Sin da Amurka su gina alaka bisa salon martaba juna da daidaito, da girmama bambance-bambancensu na tarihi, da al’adu, da tsarin zamantakewa da hanyoyin ci gaba. Kaza lika ya wajaba sassan biyu su kare moriya, da manyan abubuwan da ke jan hankalin su.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce wasu rahotanni sun ruwaito cewa, a ranar Laraba, fadar White House ta Amurka ta shaidawa manema labarai shirin sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, na ziyartar kasar Sin, inda aka bayyana cewa, Amurka na aiwatar da manufofin cudanya da kasar Sin masu dorewa, wato salon dangantakar sassan biyu yana kunshe da takara ba wai neman tashin hankali, fito-na-fito, ko sabon salon cacar baka ba.
Kaza lika Amurka na fatan ci gaba da gudanar da takara mai tsafta. Za ta kuma yi kokarin daidaita yanayin takara tare da Sin, da kuma bunkasa hadin gwiwa kan batutuwan da suka dace da burikan su.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa kan wannan batu, Wang Wenbin ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha nanata cewa, bai dace alakar Sin da Amurka ta zama ta idan bangare daya ya samu dayan ya yi asara ba, maimakon haka, dacewa ya yi sassan biyu su rika cimma nasara tare, ta yadda kowa zai iya samun riba ko hasara.
Ya ce ya kamata Sin da Amurka su rika kallon juna a matsayin abokan tafiya, a manufofin su na gida da na waje, da aiwatar da manyan tsare-tsare bisa ka’idoji, da nacewa martaba juna, da tafiya tare, bisa zaman lafiya da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Kana su lalubo hanya mafi dacewa ta kyautata jituwa tsakanin su. Hakan ne zai kare moriyar su, da ma irin fata da sassan kasa da kasa ke yi musu.
A wani ci gaban kuma, kamfanin tsaron yanar gizo na Amurka mai suna “Mandiant Corporation”, ya fitar da wata sanarwa a baya-bayan nan, wadda a cikin ta ya ce, yana zargin kasar Sin da baiwa wasu masu kutsen yanar gizo goyon baya, inda suka yi kutse cikin daruruwan na’urori masu kwakwalwa na gwamnati, da na sassa masu zaman kan su dake kasashe daban daban.
Da yake amsa tambaya game da hakan, Wang Wenbin ya ce da ma wannan kamfani ya sha fitar da irin wadannan rahotanni na karya, game da wadanda yake kira da wai “masu kutsen yanar gizo na Sin”, kuma abubuwan dake kunshe cikin rahoton kamfanin ba kamshin gaskiya ko kwarewar aiki a cikin su. (Saminu Alhassan)