Ya zuwa karshen watan Satumba da ya shude, jimillar karfin lantarki da Sin ta samar ya kai kilowatts biliyan 3.72, adadin da ya shaida karuwar kaso 17.5 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Alkaluman da hukumar makamashi ta kasar ko NEA ta fitar a Lahadin nan, sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan jiya, adadin lantarki daga hasken rana da Sin ta samar ya kai kilowatts biliyan 1.13, adadin da ya karu da kaso 45.7 bisa dari idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Sai kuma adadin lantarki daga iska, wanda ya zuwa karshen watan na Satumba da ya kai kusan kilowatts miliyan 582, adadin da ya karu da kaso 21.3 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
Kazalika, cikin watanni tara na farkon shekarar nan ta 2025, manyan kamfanonin samar da lantarki na Sin, sun zuba jarin da ya kai yuan biliyan 598.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 84.4, a fannin na samar da lantarki, karuwar da ta kai ta kaso 0.6 bisa dari a mizanin shekara-shekara.
A dai wannan wa’adi, adadin jarin da aka zuba a fannin manyan turakun dakon lantarki a kasar ta Sin, ya kai yuan biliyan 437.8, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari a mizanin shekara-shekara, kamar dai yadda alkaluman na hukumar NEA suka nuna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














