Wani matashi a Jihar Kaduna mai suna, Muhammad Salis ya koka kan halin da ya tsinci kansa sanadiyyar aiki da wani kamfanin gine-gine na kasar China da aka fi sani da CCECC da ke yi wa gwamnatin jihar aikin kwangila.
Muhammad wanda aka fi sani da Khalifa ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, kamfanin ya dauke shi aiki ne a matsayin kafinta na wucin-gadi, lokacin da yake kan yin aiki sai zarto ya yanke shi a hannu.
- An Bude Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Kasa Da Kasa Na Sin Karo Na 4
- Durkushewar Masana’antun Auduga Na Ci Gaba Da Ci Wa Al’umma Tuwo A Kwarya
Ya ce, kamfanin ya bayar da umanin kai shi asibiti don a yi masa maganin. Sai dai, ya ce a asibitin ba a yi masa allurar kashe dafi ba, wanda a hankali dafin ya shiga jikinsa ba tare da ya sani ba.
A cewarsa, bayan wani lokaci yana tsaka da aiki a kamfanin kawai sai ya yanke jiki ya fadi, inda bayan ya farfado ne sai ya ganshi kwance gadon asibiti.
Ya ce, tun bayan da aka dawo da shi gida daga asibitin iyayensa, ‘yan’uwa da abokan arziki ne ke kula da lafiyarsa.
Khalifa ya ce, likita ya shaida masa cewa sai an yi masa allurar kashe dafin ne sannan za a iya duba lafiyarsa baki daya.
A halin yanzu, hukumomin kare hakkin Dan’adam da ke Kaduna sun shiga cikin lamarin don a kwatowa matashin hakinsa daga wannan kamfanin.