Ana ci gaba da nuna damuwa a kan yadda masaku da masana’antun sarrafa auduga suka durkushe shekara da shekaru a fadin kasar nan, da kuma yadda noman auduga da ya kasance wata kafa ta samun arziki a arewa ya zama tarihi a yanzu.
A shekarun baya masana’antun sarrafa auduga (masaku) sun bayar da gudummawa sosai ga bunkasar tattalin arzikin kasa.
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
- Yawan Motocin Da Sin Ta Sayar Ya Kai Miliyan 6.72 A Rubu’in Farkon Bana
Noman auduga ya kasance wata kafar samun kudaden shiga ga manoma da ‘yan kasuwa da kuma kayan aiki ga masana’antu da masakun da muke da su a fadin Nijeriya haka kuma yana samar wa da matasa da dama aikin yi, amma kuma abin takaici a halin yanzu shi ne yadda wadannan masakun suka durkushe abin da ya yi sanadiyyar rasa ayyukan yi ga al’umma masu yawa.
Dalilai da dama suka yi sandiyyar durkushewar da aka samu wadanda suka hada da rashin ingantaccen tsare-tsare daga gwamnati, dumamar yanayi, rashin kayan aiki na zamani da kuma yadda ake shigo da auduga mai saukin kudi daga kasashen waje wanda wasu ‘yan kasuwa suka shiga yi.
Dubban manoman da suka dogara ga harkokin da suka shafi noma da sarrafa audugan sun shiga tasku haka kuma tattalin arzikin yanki ya samu koma-baya.
Binciken da LEADERSHIP Hausa ta yi, ya nuna cewa kananan kamfanonin sarrafa auduga da ke garuruwan Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara duk sun durkushe.
Haka kuma manoma a wadannan jihohin da suke samar wa da wadannan masana’antun kayan aiki duk sun yi watsi da noman saboda rashin masu hulda da su.
Misali a Jihar Kano da ake da manoman auduga fiye da 26,000 a shekarar 2019 yanzu sun ragu zuwa 24,500 a shekarar 2020. Yawancinsu sun amfana da shirin bashi na ‘Anchor Borrowers’’ da CBN ya bayar.
A tattaunawarsa da LEADERSHIP Hausa, shugaban kungiyar masu noman auduga ta Nijeriya, reshen jihar Kano, Ibrahim Abdulhamid ya bayyana cewa, “A shekarar 2019, lokacin da gwamnmati ta bayar da tallafin aikin noma, an samu manoma 26,000 amma a shekarar 2020, adadin wadanda suka shiga shirin ya koma 24,500 amma a halin yanzu da wuya ka samu manoma 2,000 da ke harkar noman auduga a Jihar Kano. Binciken da muka yi a wasu jihohin ya nuna lamarin kusan duk daya ne.
Saboda a halin yanzu Nijeriya ta sauko a matsayinta na shugaba a Afrika ta masu noman auduga.
Wani rahoto da aka wallafa a kafar ‘mordorintelligence.com/industry-reports/africa-cotton-market’ ya nuna cewa, yawancin kanana manoma ne ke a kan gaba wajen noman auduga, duk da ana samun wasu manyan gonaki, hakan na faruwa ne saboda yawanci ana noma auduga ne a matsayin hanyar samun kudin shiga, kuma a halin yanzu babu kasuwar.
Wani abin lura kuma shi ne kasashe kalilan ne a Afrika ke amfani da ingantattun irin auduga da aka alkinta, sun kuma hada da kasashen Afrika ta Kudu, Sudan, Barkina Faso a nan ne kuma ake samun manoman da suke amfani da irin audugan da aka alkinta wadanda ke bayar da yabanya mai yawa.
Bincike ya nuna cewa, kasashen Mali, Burkina Faso, da Kwadebuwa ke a kan gaba wajen samar da auduga a Afrika inda suke bayar da kashi 50 na audugan da ake da shi a yankin Afrika gaba daya.
Kasashe da suka fi sayen auduga daga Afrika sun hada da Bangladesh, Bietnam, da Malaysia. An fi samun samun auduga ne a yanayi mai dumi da kasa mai damshi shi ya sa yankin Saharan Afrika ya kasance wurin da aka fi noma auduga a duniya gaba daya.
A jawabinsa, shugaban hukumar kula da harkar gona ta Jihar Kano, Gambo Isa Garko, ya tabbata da raguwar harkar noman auduga a jihar inda ya alakanta hakan a kan rashin ingantattun irin shukawa da kuma farmakin kwari.
Ya ce, audugan da aka fi nomawa a lokacin damuna ya samu bunkasa ne a jihar a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin ‘anchor borrowers’ don tallafa wa manoman auduga a kasar nan.
A cewarsa a lokacin da manoma suka samu tattalin an samu karuwa noman auduga amma a lokacin da aka dakatar da tallafin noman audugan ya tsaya cik.
“A lokacin an tallafa wa kamfanoni domin su farfado da ayyukansu, amma daga karshe kamfanonin sun kasa ci gaba da aiki saboda ba zai yiwu su sayar da kayan su a farashin da ya dace ba saboda yadda suke samun kayan tun da farko a kan haka suma manona suka dakatar da noman audugan saboda rashin masu saya, musamman kuma rashin ingantaccen farashi.
“A kan haka yawacin kamfanonin da ke da alaka da harkar masaku suka daina aiki abin ya kai ga kamfanoni masu samar da sinadarai duk suka durkushe gaba daya.
“Ya ce, saboda babu isasun manoman da za su samar wa kamfanonin auduga kayan aiki, wadannan ne matsalolin da suka hadu suka yi wa harkar katutu.
Lamarin duk daya ne a ta bakin shugaban kungiyar masu noma auduga na (NACOTAN), Ibrahim Abdulhamid, ya kuma kara da cewa, matsalolin da harkar noman auduga ya fuskanta har aka samu ragowa da kashi 70 sun hada da rashin cikakken sanya kudi daga gwamnati da rashin malaman gona masu bayar da shawarwari da mastalar tsaron da ake fuskanta a wasu sassan yankin arewa. Ya ce yankuna irinsu kananan hukumomin Karaye da Gwarzo da suke a tsakanin iyakokin Jihar Katsina suna fuskantar matsalolin ‘yan bindiga wanda hakan ya hana su shiga harkar noman samar da auduga.
Darakta a ma’aikatar masana’antu da zuba jari na jihar Kano, Mamoud Bala, ya nuna takaicinsa a kan yadda masana’antun masaku da dama a Jihar Kano suka durkushe gaba daya. Ya ce, a baya wurare irinsu Bompai, Sharada, da Chalawa sun kasance fagen da manyan masaku suke harkokinsu amma a halin yanzu duk sun durkushe.
Ya kuma dora alhakin wannan ne a kan rashin isasshen wutar lantarki, fasakwauri da shiga da kayayyaki da kasar Chana da wasu kasaashe duniya.
Masakun da aka farfado da su a Katsina ba sa aiki yadda ya kamata
A kokarin farfado da noma auduga domin samun abubuwan da masana’antu za su yi amfani da su, gwamnatin Jihar Katsina ta farfado na noman rani a fadin jihar gaba daya don samar da auduga.
Wannan na daga cikin tsare tsaren gwamnan jihar Dikko Umaru Radda na shigo da aikin gona na zamani don samar da kudaden shuiga da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Shugaban kungiyar manoma ta ‘All Farmers’ Association of Nigeria (AFAN), Umar Ya’u Gwajo-Gwajo, wanda ya sanar da haka a tattunamawarsu da wakilinmu, ya kara cewa, gamnatin jihar ta fito da wasu shirye-shirye na samawar wa da manoma kayan aiki na zamani ta hannun kungiyar don kara bunkasa harkar noma a fadin jihar.
Ya ce, an shirya amfani da manoman auduga ne don amfanar manoman da gwanmnati da kuma bukatar farfado da masana’antun da muke da su a fadin jihar, a kan haka gwamnati ta dauki ma’aikatan gona don cimma nasarar wannan shirin.
Manoman Jihar Kwara Sun Nemi Tallafin Gwsmanati A Kan Noman Auduga
A halin yanzu kuma manoman auduga a Jihar Kwara sun nemi gamnatin jihar ta tallafa musu da kayan aki kamar takin zamani don inganta aikin su.
Manoman audugan da aka fi samu a yankuna kananan hukumonin Kwara North da Kaiama sun mika wannan bukatar ne a tattaunawarsu da LEADERSHIP Hausa a babban birnin jihar Ilorin.
Sun bayyana wannan bukatar ne a ta bakin shugaban kungiyar manoman Jihar Kwara, Hon. Umar Mahmud Aboki, wanda kuma yana cikin manya-manyan manoman auduga na Jihar Kwara.
Ya kara da cewa, babu kamfanoni masu sarrafa auduga a jihar amma wasu mabukata daga wasu jihohin arewa suke shigowa don sayen audugan da aka noma.”
LEADERSHIP Hausa ta lura da cewa, masaka daya tilo da ke jihar Kwara ta daina aiki ne tun zamanin mulkin sojoji a Nijeriya.
Haka kuma mai ba gwamnan shawara na musamman, a kan harkokin yada labarai, Alhaji Bashir Adigun ya ce, gwamnati na taimaka wa dukkan manoma a jihar ciki har da manoman auduga da taki da kuma ingantaccen iri don inganta harkar noman su.
Labarin kusan daya yake a jihohin Sakwkato, lamarin noman auduga ya ja da baya sosai a ‘yan shekarun nan. A ta bakin Sani Tangaza wani dan shekara 54, ya bayyana yadda ya samu mahaifinsa marigayi Alhaji Sani Abdullahi, a harkar saye da sayar da auduga, inda yake kasuwancin auduga daga nan zuwa garin Futunwa ta Jihar Katsina amma a halin yanzu lamarin ya zama labari.
“A yau dai muna da filayen noma amma harkar noma ya tsaya tun daga lokacin da masana’antun masaku suka durkushe.
Da yawa daga cikin wadanda suka tattunawa da jaridar EADERSHIP sun nemi gwamnatin jihoji 19 na arewacin kasar nan su hada hannu wajen farfado da masana’antu da harkar noman auduga a kasar nan ta hanyar samarwa da manoman tallafi na musamman na kayan aiki na zamani.
Sun ce, farfado da harkar noman auduga a kasar nan za ta taimaka wajen samar da aikin yi ga al’umma sannan za ta taimaka wajen samar da aikin yi ga dimbin matasanmu.