• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aikin Gine-gine Na Kasar Sin Suka Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka

by CGTN Hausa
2 years ago
Gine-gine

A jiya Asabar ne aka kaddamar da gasar cin kofin nahiyar Afrika karo na 34 a Abidjan, babban birnin harkokin tattalin arziki na kasar Cote d’Ivore, inda kuma aka gudanar da wasan farko na gasar a filin wasa na Alassane Ouattara dake birnin na Abidjan, filin wasan da kasar Sin ta ba da gudummawar ginawa.

Za a shafe kusan wata guda ana fafatawa a gasar wadda za ta gudana a filayen wasa 6 dake birane 5 na Cote d’Ivore, kuma kamfanonin kasar Sin ne suka gina wasu daga cikin filayen wasan da suka hada da na Korhogo da na San Pedro, wato baya ga filin wasa na Alassane Ouattara.

  • Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi Al’ummomin Bwari A Abuja
  • Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi Al’ummomin Bwari A Abuja

Daidai kwanaki biyu kafin bude gasar kuma, aka bude wata gada da kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina, wadda za ta rage cunkoso a titunan Abidjan, yayin da dubban dubatar masoya kwallon kafa daga sassan duniya ke zuwa kasar domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 34. A ranar 10 ga wata, firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Mambe ya duba ingancin gadar, inda ya bayyana aikin gadar a matsayin wani muhimmin shiri na samar da ababen more rayuwa, wanda ya zama muhimmiyar hanyar sufuri don kyautata zirga-zirga a babban birnin kasar Abidjan.

Hakika, filayen wasa da kuma gada da kasar Sin ta gina a kasar Cote d’Ivoire, wani bangare ne kadai na yadda kasar Sin ke taimakawa wajen gina manyan ababen more rayuwa a kasashen Afirka. Amma mene ne dalilin ta na yin haka? Sabo da kasancewar Sin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, ban da dankon zumunci da ke tsakaninsu, suna kuma fahimtar juna. Sakamakon yadda kasar Sin ta san muhimmancin ababen more rayuwa ta fannin ci gaban kasa, shi ya sa take iya kokarin aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyoyi daban daban, don inganta ababen more rayuwa a kasashen, da ma kwarewarsu wajen raya kansu da tabbatar da dauwamammen ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Bisa ga tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kawo yanzu kamfanonin kasar Sin sun gina layukan dogo a Afirka da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10, baya ga hanyoyin mota da suka kai kusan kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan dari, da ma dimbin asibitoci da makarantu da filayen wasa.

Na san da yawa daga cikinku masu sha’awar wasan kwallon kafa ne, to me zai hana ku je wajen gasar cin kofin Afirka da ke gudana a Cote d’Ivoire? Ina da imanin gada da ma filayen wasan da kasar Sin ta gina za su kara sa ku jin dadin gasar. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Next Post
AFCON 2023: Nijeriya Ta Buga Canjaras Da Kasar Equatorial Guinea

AFCON 2023: Nijeriya Ta Buga Canjaras Da Kasar Equatorial Guinea

LABARAI MASU NASABA

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

November 3, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

November 3, 2025
Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

November 3, 2025
2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.