• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Ƙaddamar Da Manyan Ayyukan Tituna A Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara

by Leadership Hausa
1 year ago
ayyuka

A ranar Juma’ar nan ne Gusau babban birnin Jihar Zamfara ta ƙara samun tagomashi yayin da tsohon Gwamnan Bauchi, Ahmed Adamu Mu’azu ya ƙaddamar da wasu ayyukan tituna da Gwamnatin Dauda Lawal ta kammala cikin shekara guda da karɓar mulki.

Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu wanda yake tsohon Shugaban PDP na ƙasa, ya jinjina wa Gwamna Dauda Lawal bisa ayyukan inganta tituna da yake aiwatarwa.

Mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa titunan da Adamu Mu’azu ya ƙaddamar, sun haɗa da titin Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist; sai kuma wacce ta tashi daga Freedom Square zuwa gidan gwamnati; da kuma ta gidan gwamnati zuwa Lalan zuwa Gada Biyu.

ayyuka

Idris ya ƙara da cewa ayyukan titunan Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist, da ta Freedom Square zuwa gidan gwamnati, kamfanin Ronches Nigeria Limited ne ya aiwatar da su; sannan shi kuma kamfanin Triacta Nigeria Limited ya aiwatar da titin da ya tashi daga gidan gwamnati zuwa Lalan zuwa Gada-Biyu.

LABARAI MASU NASABA

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

Cikin jawabinsa wajen bikin, Gwamna Dauda Lawal ya bugi ƙirjin cewa tun da aka kafa jihar Zamfara, shekaru 28 ke nan, sai yanzu ne Gusau ta cancanci a kirata babban birnin jihar.

“Zan fara da yi wa babban baƙon mu marhabin lale zuwa wannan biki. Wannan kuwa ba wani ba ne illa Tshohon Gwamnan jihar Bauchi, kuma Tshohon Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, mai girma Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, CON. Har gobe abubuwan da ka kafa a matsayin ka na Gwamna da shugaban PDP, zai zama abin koyi ga shugabanni masu tasowa.

ayyuka

“Babu shakka, dole ne mu yi wa Allah godiya mara iyaka bisa damar da ya ba mu na aiwatar da ayyuka, uwa-uba, Allah ya ba mu damar cika alƙawuran Zamfarawa da muka ɗauka a lokacin yaƙin nemam zaɓe. Ina ƙara jaddada aniyata ta sadaukarwa ga jihata a kowane lokaci.

“Don haka, bisa waɗannan ni’imomi na Allah, yau za mu buɗe hanyar da ta tashi daga Freedom Square zuwa mahaɗar Nasiha Chemist, Freedom Square zuwa gidan gwamnati, wanda kamfanin Ronches Nigeria Limited ya aiwatar; sannan daga gidan gwamnati zuwa Lalan Gada-Biyu, shi kuma kamfanin Triacta Nigeria Limited ne ya aiwatar. Waɗannan na ciki wasu ayyukan da gwamnatina ta aiwatar daga lokacin da muka hau mulki.

“Waɗannan ayyuka da muke ƙaddamarwa a yau, kashi na biyu ne a jerin ayyukan mu masu ɗimbin yawa. Da zarar mun kammala tsare-tsaren da muka yi na raya birane, to dukkan mu za mu iya bugun ƙirji mu kira Gusau a matsayin babban birnin jihar mu. Bugu da ƙari, za mu aiwatar da ayyukan more rayuwa a duk Ƙananan Hukumomin jihar nan 14.

ayyuka

“Da wannan ɗan taƙaitaccen jawabin, na ke farin cikin gayyatar Tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, CON, ya zo ya buɗe waɗannan ayyukan da gwamnatina ta aiwatar a shekara ɗaya da na yi ina shugabantar jihar nan, a matsayin wani sashe na ayyukan raya birane.”

Tun farko, Babban baƙo, Tsohon Gwamnan jihar Bauch, Alhaji Ahmad Adamu Mua’azu, CON, ya nuna matuƙar jin daɗin sa bisa waɗannan ayyukan na Gwamna Lawal, yana mai bayyana cewa shi shugaba ne mai ƙwazo da hangen nesa.

“A yau, ina mai alfahari da godiya ga Allah bisa ayyukan yabawa da Gwamna Dauda Lawal ya aiwatar.

“Babban al’amari na waɗannan titunan shi ne cewa an gina su da inganci kuma bisa tsarin yadda duniya ke tafiya. Zan iya tabbatar muku da cewa waɗannan hanyoyi ne masu ɗorewa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
Labarai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja
Manyan Labarai

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
NAWIA
Labarai

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Next Post
Laifukan Shafin Intanet Na Ci Gaba Da Ci Wa ‘Yan Nijeriya Tuwo A Kwarya

Laifukan Shafin Intanet Na Ci Gaba Da Ci Wa 'Yan Nijeriya Tuwo A Kwarya

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.