• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Gudanar Da Hawan Daba A Ƙauran Namoda Da Naɗa Gwamna Dauda Sarauta

by Leadership Hausa
2 years ago
Hawa

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Daba a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a ranar Lahadin nan.

Masarautar Ƙauran Namoda na gudanar da wani gagarumin biki na musamman bayan Sallar Idi, wanda aka fi sani da Hawan Durbar duk shekara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, bikin hawan Durbar na haɗa jama’a domin murnar zagayowar ranar sallah da kaɗe-kaɗe, raye-raye, da sauran al’adun gargajiya.

Sanarwar ta ce, a yayin bikin hawan Durbar mai ban sha’awa, an naɗa Gwamna Lawal sarautar ‘Wakilin Kaura’, wanda ke nufin wakilin wanda ya kafa masarautar.

  • Yanzu-yanzu: Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da Matasa A Gashuwa

LABARAI MASU NASABA

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

“Gwamna Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Daba na Masarautar Ƙauran Namoda a yau.

“Hawan Daba wani biki ne mai ban-sha’awa wanda ke nuna al’adun gargajiyar masarautar Ƙauran Namoda. Hawan Durbar da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda tana bai wa jama’a damar haɗuwa waje guda, tare da taya murna zagayowar sallar wannan shekara.

“Bikin Daba na bana ya zama mai matuƙar muhimmanci ga masarautar, domin wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci a jihar ya halarci taron.

“Gwamna Lawal, sanye da kayan gargajiya, ya shiga hawan Daba a lokacin da yake kan dokin da aka ƙawata da kayan ado.

Hawa

“A lokacin da ake gudanar da bikin, Sarkin Ƙauran Namoda, wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda, Dokta Sanusi Muhammad Ahmad Asha ya bai wa Gwamna Dauda Lawal sarautar gargajiya ta Wakilin Ƙaura, wato wakilin wanda ya kafa masarautar. Wannan karimcin ya nuna godiya ga halartar gwamnan a wajen bikin.”

Sannan Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da ƙofar birnin Modomawa, tsohuwar ƙofar Kauran Namoda tun daga 1807-1810.

Ya kuma duba cibiyar kula da gidan talabijin ta Nijeriya NTA a Ƙaramar Hukumar, inda ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafin da ya dace don farfaɗo da tashar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka
Labarai

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Hawa
Manyan Labarai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
Next Post
Bangaren Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin Ya Yi Kira Ga EU Da Ya Gudanar Da Bincike Bisa Adalci

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.