Taron ranar hausa ta duniya taro da majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 26 ga watan Agusta domin raya ta a duk fadin duniya.
To, sai a wannan karon taron ya sam u tagomashi inda masarautar Daura hadin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina suka shirya shi domin bunkasa harshen Hausa da kuma Hausawa.
- Ranar Hausa: Masana Sun Bayyana Bunkasa Da Tasirin Harshen A Duniya
- Shugaban NPA, Dantsoho Ya Zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Tashoshin Ruwa Ta Duniya
Taken taron na wannan shekara ta 2025 shi ne “yin amfani da harshen Hausa wajen wanzar da zaman lafiya” kamar yadda aka bayyana tun kafin wannan rana.
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.
Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.
Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa.
Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta duniya.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan sun hada da gwamnan mulkin Soji na jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci ya jagoranta tare da mai martaba Sarkin Damagaram Sultan Abubakar Umar Sanda
An fara bude taron addu’a sannan fara baje kolin al’adu da sana’o’in Hausawa inda aka fara shakatawa da wanzamai bayan sun nuna ta so bajintar da kwanji da kuma makera wadanda suka yi wasan wuta a gaban dubun dubatar jama’ar da suka halarci taron.
Kazalika an yi wasan kokawa wanda shi ne ya kayayar da mahalarta taron, inda daga bisani aka shirya gagarumar daba ta hawan dawakai da ‘yan tauri da masu algaita da sauran su.
An shirya hawan dabar ne tamkar yadda masarautar Daura take shirya hawan Sallah ko Sallar Gani inda aka jero garuruwan Hausa bakwai da kuma kanne bakwai (tsohuwar banza bakwai)
Bayan kammala wannan daba da nuna al’adun gargajiya na bahaushe da hausawa an gudanar da jawabai daga manyan baki da suka halarci wannan taro na habaka harshen Hausa.
Sanata Ibrahim Ida Wazirin Katsina na daga cikin wadanda suka yi jawabi inda ya fara nuna mahimmancin da Majalisar dinkin Duniya ta baiwa harshen Hausa, al’adu da kuma adabin Hausawa a idun duniya.
Wazirin Katsina ya cigaba da bayanin cewa abu ne mai mahimmanci a fahimci cewa harshen Hausa na daga cikin manyan harsuna da ake amfani da su wajen magana, da sauran mu’amula ta yau da kullum.
Sanata Ibrahim Ida ya bayyana cewa yanzu an tabbatar da cewa harshen Hausa ya fi kowane harshe a Afrika yawan masu yin magana da shi da kuma yin huldodin rayuwa na yau da kullum.
Abdul Baki Jari na daya daga cikin wadanda suka assasa wannan rana ta ranar Hausa ta duniya wanda majalisar dinkin duniya ta amince a shekarar 2015.
Ya kara da cewa babban makasudin wannan taro shine domin a sada zumunci a tsakanin Hausawa da ke kasashe fiye da 25 a fadin duniya inda yanzu haka ana cigaba da irin wadannan bukukuwa.
Abdul Baki Jari ya nuna bukatar da ake da ita wajen gudanar da bincike akan makomar harshen Hausa da ke fuskantar kalubale a wasu kasashe.
Haka kuma ya nuna godiya da farin ciki da kasashe da suka halarci wannan taro musamman kasashen Camerou da Chadi da Ghana da Barkina Faso da sauran kasashen duniya wadanda aka ke tara ruwa kafin azo nan.
Shima da yake nasa jawabi wakilin shugaban kasar jamhuriyar Nijar kuma gwamnan jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci ya nuna godiya da fatan ga wadanda suka shirya wannan taro.
Kanal Massallaci ya bayyana cewa irin wadannan tarurruka shugaban kasar Nijar Janar Abdurrahaman Tiachni ke bukata domin ganin an hada kan hausawa wuri guda.
“Ya zama wajibi Hausawa su farka daga dogon barcin da suka yi, idan aka duba yanzu Hausawa sun fara barin gadon su, to ya zama dole a koma ma gado da al’adu irin wannan aka hada Iyaye da kakanni” in ji shi
Gwamnan Damagaram din ya yi fatan ya a rika amfani da irin wadannan tarurruka nan gaba domin kara dankon zumunci tsakanin kasashen Afrika inda nan ne Hausawa suka fi yawa.
Daga wadanda suka halarci wannan taro sun hada da gwamnan jihar Damagaram Kanal Muhammad Sani Massallaci da Mai martaba Sarkin Damagaram Sultan Abubakar Umar Sanda da Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida da Sardaunan Kasar Hausa Mai tuta Hon. Alasan Ado Doguwa.
Sauran sun hada da wakilin gwamnan jihar Katsina kuma mai baiwa gwamna shawara akan harkokin masarautu Alhaji Usman Abba Jaye da sauran masu rike da masarautar da hukumomi.