A ranar Asabar na makon jiya ne Cbiyar Yusufu Bala Usman ta shirya taron masana da suka fito daga sassan kasar nan inda suka gabatar da mukala daban daban a kan irin rayuwa da gwagwarmayar da Marigayi Dr Bala Usman ya yi a lokacin rayuwarsa, ya kuma rasu ne shekara 20 da suka gabata.
Cikin shahararrun masanan da ke kan gaba wajen gabatar da bayanai a wajen taron sun hada da Farfesa Attahiru Jega, Farfesa Iyochia Ayu, Farfesa Jerome da kuma Dr Auwalu Anwar da Ambasada Abdul Zango.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Saliba Ya Sabunta Kwantiraginsa Da Arsenal Har Tsawon Shekaru 5
Bayanan nasu ya fito da irin gudummawar da Bala Usman ya bayar ne a cikin littatafan da ya rubuta da kuma akidojinsa na yadda ya kamata a tafiyar da rayuwar al’umma cikin nasara.
A nasa tsokacin Dr Auwalu Anwar ya ce, lallai da Bala Usman zai dawo duniya a yanzu bayan shekara 20 da rasuwarsa da zai nuna bacin ransa a kan irin kungiyoyin siyasar da muke dasu a Nijeriya. Ya kara da cewa, Bala Usman yana mai fatan samun jami’iyyun siyasa da suka samu asali ne daga kokari da fafutukar talakawa, sune kuma suke gudanar da ita ba manyan masu kudi ba wadanda ke amfani da jami’iyyun domin kaiwa ga madafun iko.
Shi kuwa Ambasada Abdul Zango ya bayyana irin gudummwar da Bala Usman ne ya bayar wajren samar wa kasar nan alkiblar yadda za ta tafiyar da harkokin hulda da kasashen waje. Ya ce marigayi Bala Usman ne ya rubuta wa marigay shugaban mulkin soja na kasar nan Murtala Mohammed jawabin da ya yi a taron kungiyar kasashen Afrika ta OAU wanda ya gudana a kasar Addisa Baba, jawabin da ya shahara a duniya. Ya kuma bayyana cewa, in har da Bala Usman zai dawo ya ga yadda ake tafiyar da harkokin kasashen waje na Nijeriya a halin yanzu lallai ba zai ji dadi ba saboda yadda ake tafiyar da it ba tare da kishin kasa da akida ba.
Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp