- Munakisa Ce Ta Kayar Da Tinubu, Cewar El-Rufai
- Dama Damfara Ce Kawai, In Ji Hamza Al-mustapha
- PDP Ta Yi Damarar Cin Gajiyar Abin
Kafin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN su amince da kara wa’adin daina karbar tsofafin takardar naira 200, 500, da naira 1,000 da aka sauya wa fasali zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu 2023 al’amurra sun dauki zafi bangaren tattalihn arziki da zamantakewar al’umma Nijeriya sun nemi tsayawa ciki kasuwannin da suke ci mako mako sun kulle, zirga-zirgar motoci sun tsaya.
Ba a wannan karon aka fara canza fasalin kudi a Nijeriya, shugaba Buhari a lokacin da ya jagorancin Nijeriya a matsayin soja a shekara 1983 ya yi canjin kudi wanda ‘yan Nijeriya da dama suka tafka asara sabosa kasa cimma wa’adin mayar da tsofaffin kudin zuwa banki wannan ya sa wadanda suka san irin dambarwar da aka fuskanta a waccan lokacin suka shigta dimuwa da fargabar halin da za a iya shiga in har wa’adin ya kulle mutum bai kai kudinsa banki ba.
Canjin kudi na wannan karon ya zo da sabon salo ne musamman ganin ya zo ne ana tsakiyar hadahada da gangamin siyasar 2023, kuma kowa yana sane da cewa, harkar siyasa a kasar nan abu ne da ya yake tafiya da kudi, ma’ana iya kudin ka iya shagalin ka, yawan kudin ka shi e yawan irin mutanen da za ka iya tarawa a gangamin siyasarka, sai ga shi kudi ya yi karanci a hannu manya da kananan ‘yan siyasa, wannan kuma shi ne ya sa wasu masu lura da al’amurran yau da kullum ke ganin babban makasudin kirkiro da sauya fasalin nairar ma tunda farko ya zo ne saboda a dakike shirin da wasu ‘yan siyasa suka saba yi na sayen kuri’a a ranar zabe, an shirya samar da kamfar kudi nne don wadanda suka shirya yin amfani da kudi wajen karkatar da ra’ayin masu jefa kuri’a daga abin da suka shirya zaba tunda farko.
Wannan canjin ya kara fito da wasu boyayyun abubuwa a filin Allah, al’amurrar sun kuma hada da gazawar hukumar Babban Banki Nijeriya na tanadar isssasun sabbin kudin a bankuna, duk da cewa, shugaban babban bankin CNB ya karyata wannan batun, yana mai cewa, an samar da isasshen kudi a banku nan mu, sune ke kin zuwa karba ku kuma in sun kaubo sai su karkatar dasu zuwa wasu bangarorin, aka bar mutane na ta shan wahala.
Wananan hali na dimuwa da tashin hankali da mutane suka shiga wanda ta kai ga suna yin Allah wadai da gwamnati a kan jefa su halin kunci da tashin hankali, har ma wasu na ikirarin ba za su zabi jam’iyya mai mulki ba, abin da ya sa dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Biola Ahmed Tinubu ya bara, yana mai korafin cewa, an kikiro da lamarin canjin ne tun da farko don kawo masa cikas a yunkurinsa na zama shugaban Nijeriya, wanna korafin ce ya sanya ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP ta yi amfani da dama wajen kira ga al’ummar Nijeriya su kaurace wa jam’iyyar APC musamman ganin irin halin da al’amarin canji ya jefa al’umma.
Masu lura da al’amurran yau da kullum suna da ra’ayin cewa, rahoton da aka samu na jifar tawagar shugaban kasa a yayyin da ya kai ziyara garin Katsina don kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da
Gwamna Masari ya yi da kuma yadda kasance a yayin da Shugaba Buhari ya kai ziyarar kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da Gwamnan Ganduje ya yi a Jihar Kano, labari ya nuna yadda wasu yara ke jifa suna kuma furuce-furucen “Bama yi! Bama son canji, da sauransu. Tabbas a bayyane yake cewa, al’amarin canjin nan ya kara wa gwamnatin Shugaba Buhari karin bakin jini ne, mutane da ganin cewa, da gangan aka haifar da karancin kudin a daidai wannan lokacin da mutane ke fuskantar jerin matsaloli daga bangarorin rayuwa. Haka kuma karancin mai da ake fuskanta duk suna cikin al’amurran da suka karawa gwamnatin bakin jinin wanda jam’iyyun siyasa suka shiga amfani da su wajen nemawa kansu karin magoya baya da kuma dakile farin jinin jam’iyyar gwamnati mai mulki.
A wata sabuwa kuma, Da yake bayani a wani zauren tattauna wanda wasu shaharrun Lauyoyi da ‘yan Jarida ke gabatarwa a shafin intanet, Manjo Hamza Al-mustapa (Mai Ritaya) yana cewa, canjin kudn da aka yi ba komai ba ne illa damfara, yana mai cewa, “419 (Damfara) aka shirya domin a wahalar da ‘yan Nijeriya, idan kuma Emifiele ya isa, ko shi, ko mukarrabansa su fito fili su karyata in ban tona asiri ba” in shi ji.
Haka kuma Gwamnan JIhar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa, akwai wasu a fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da suke neman kayar da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
El-Rufai ya sanar da haka ne a tattaunawar da ya yi da gidan talabijin na Channels a shirin ‘Breakfast show’’ ‘Sunrise Daily’ ranar Laraba a Abuja.
Ya kara a cewa, wasu a fadar shugaban kasa suke shirya munakisar,suna neman yi wa dan takarar shugabancin kasa na APC zagon kasa saboda ba gwanin su ne ya ci zabe ba a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi ba a kan haka suke ganin lallai sai Tiubu ya fadi zabe.
Idan za a iya tunawa a makon jiya ne aka ruwaito, dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kalubalanci gwamnatin tarayya a kan kirkiro da shirin sauya fasalin naira da kuma karacin man fetur da ake fuskanta yana mai cewa, duk an kirkiro ne don kawo wa shirinsa na eman shugabancin kasar nan a zaben 25 ga watan Fabrairu cikas.
Ana cikin halin dimuwa na yadda za a fuskanci rayuwa a daidai lokacin da aka kulle karbar tsofaffin kudaden don kuwa masana harkar tattalin arziki sun yi has ashen irin matsalolin da za a shiga da irin asarar da za a tafka, sai kuma ga sanarwa daga Babban Bankin Nijeriya CBN ya kara wa’adin karbar canjin kudi zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, wannan kuma ya samu ne bayan da aka ruwaito cewa, dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa wajen Shugaba Buhari in da ya yi magiya tare da neman alfarmar lallai a kara wa’adin karbar tsofaffin kudaden da aka sauya wa fasali, a wanna ana fatan zai rage dimuwa da fargabar da al’umma suke ciki zai kuma rage cunkoso da ake fuskanta inda zaka ga dogayen layukan mutane a bankuna kasar nan suna neman a canza musu tsofaffin kudaden su, su kuma wasu bata garin ‘yan Nijeriya na amfani da wannan damar suna zaluntar mutane ta hanyar karbar wasu kudi kafin su canzar musu da sabbin kudin.
Daga dukkan alamu ‘yan Nijeriya za su ci hawa layuka daban daban don biyan bukatun rayuwarsu, layukan da suka hada da layi a gidajen man fetur, layi a bankuna don neman canjin kudade ga kuma layin karbar katin zabe, layin kuma da za a fuskanta a nan gaba kada shi ne layin kada kuri’a a ranar ranar 25 ga watan Fabrairu a wannan shekarar 2023.