Murabus din, a jiya, na Alkalin-alkalai a ranar Litinin, Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, shiri ne mai rudani da aka dade ana shirya masa amma ba ayi nasara ba sai a daren Lahadin da ta gabata, kamar yadda wasu majiyoyi da ke da alaka da siyasa suka shaida wa kamfanin Daily trust.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa sabanin tunanin da mutane ke yi na cewa Alkalin-alkalai Muhammad ya yi murabus ne da kan sa, hakika wasu manyan jami’an tsaro da manyan jami’an gwamnati ne suka tilasta masa yin hakan.
An fara gane alamun Murabus din Tanko ne a safiyar ranar Litinin yayin da yaki halartar wani taro wanda shine zai yi jawabi a wajen bude taron kan horar da alkalai kan hanyoyin warware rikici, a cibiyar shari’a ta kasa (NJI) da ke Abuja.
Ba a ga Alkalin-alkalai Muhammad Tanko a wurin ba, bai aiko da wata sanarwa ko wakili ba.
Sannan Mataimakansa sun ce ba su da wata masaniya kan shirin yin murabus ba, sai da safe.
Sai dai wasu majiyoyi sun Bayyana cewa an umarce shi ne da ya bayyana a fadar Shugaban kasa inda aka tilasta masa sanya hannu kan takardar murabus din.
Bayan murabus din Muhammad, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda shi ne na biyu a kotun koli a matsayin mukaddashin Alkalin-alkalai.