• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

by Abba Ibrahim Wada
5 hours ago
Gasa

Kamar yadda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF ta tsara, za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin na Afirka.

Kuma wannan shi ne karon farko tun bayan 1988 da Morocco za ta karbi bakuncin wasannin babbar gasar kwallon kafa ta duniya da take fatan gudanar da bikin da zai kayatar da duniya.

  • An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

A wannan lokacin hankula za su karkata kan kasar da take Arewacin Afirka, wadda take cikin hadakar gasar kofin duniya a 2030. Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025 na tattare da kalubale, fiye da wadanda aka yi daga shekara 10 zuwa 15 baya, inda tawaga 24 za ta kece raini a filayen wasa tara cikin biranen kasar guda shida.

Kamar yadda aka sani a baya ana buga gasar tsakanin Yuni zuwa Yuli, amma a gasar bana za a yi ne cikin watan Disamba, saboda wasannin gasar kofin duniya da za a yi a 2026 daga 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Medico.

Amma dai gasa biyu an yi tsakanin Janairu zuwa Fabrairu, amma wadda za a gudanar a 2025, an tsara yi daga Disamba zuwa Janairun 2026 kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

LABARAI MASU NASABA

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa.

Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman mataki na uku da kuma wasan karshe.

 

Yadda aka raba rukunan gasar

An raba tawaga 24 da za ta buga gasar kofin Afirka zuwa rukuni shida dauke da hurhudu kowanne.

 

Rukunin A : Morocco, Mali, Zambia, Comoros. Rukunin B : Masar, Afirka ta Kudu, Angola, Zimbabwe

Rukunin C : NIjeriya, Tunisia, Uganda, Tanzania. Rukunin D : Senegal, Jamhuriyar Congo, Benin, Botswana. Rukunin E : Algeria, Burkina Faso, Ekuatorial Guinea, Sudan. Rukunin F : Ibory Coast, Kamaru, Gabon, Mozambikue

 

Kasashen da ake hasashen za su iya lashe gasar Morocco

Ita ce ta farko daga Afirka da ta kai zagayen daf da karshe a tarihi a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Katar a 2022. Saboda haka tana sahun gaba da ake gannin za ta iya lashe kofin Afirka da take karbar bakunci. Rabon da kasar ta lashe kofin tun 1976, saboda za ta yi fatan daukar karo na biyu.

A gasar da aka yi a 2024, an yi waje da Morocco a zagaye na biyu wato ‘yan 16

Senegal

Mai rike da kofin 2022 za ta buga wasannin da kwarin gwiwa mai tarin fitattun ‘yan wasa da ke buga wasa a faɗin duniya karkashin Pape Thiaw, wanda ya maye gurbin Aliou Cissé. Senegal tana tare da tsoffin ‘yan wasanta da kuma matasan da suka hada da Sadio Mané da Kalidou Koulibaly da Edouard Mendy da Gana Gueye da Nicolas Jackson da Pape Matar Sarr da Habib Diarra da kuma Iliman Ndiaye.

Kawo yanzu Senegal ce kan gaba a yawan wasa ba tare da rahin nasara ba a duniya guda 25 sai Afirka ta Kudu da 23 da kuma Sifaniya mai wasa 22, Masar

Kasar Masar mai kofin Afirka bakwai tana cikin wadanda za su iya lashe kofin, wadda take karkashin Hossam Hassan ta yi wasa 12 a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba. Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Mohamed Salah yana daga fitattun ‘yan wasan tawagar da ake sa ran za su nuna kansa a wasannin.

 

Algeria

Mai koyar da tawagar ‘yan wasan kasar, Bladimir Petkobic yana ta kokarin ganin ya mayar da kasar kan ganiya, mai fitattun ‘yan wasa Mahrez da Slimani da kuma matasa Mohamed Amoura da Anis Hadj Moussa. Bayan da aka yi waje da Algeria karo biyu a jere bayan wasannin cikin

rukuni, kasar na fatan yin abin kirki a Morooco, kuma rabonta da kofin Afirka tun 2019.

 

Ibory Coast

Kasar Ibory Coast ce mai rike da kofin za ta yi kokarin sake lashe kofin karashin Emerse Faé. Duk da cewar ta yi rashin nasara a hannun Saliyo da Zambia, tawagar za ta Morocco da fitattun ‘yan wasa, illa dai akwai kalubale a matakin mai rike da kofin Afirka. Ibory Coast ce ta dauki kofin karo biyu daga gasar takwas a gasar cin kofin duniya daga cikin tawagogin da za su kece raini a Morocco.

 

Nijeriya

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya wadda ta yi ta biyu a gasar da aka buga a Ibory Coast, za ta shiga wasannin da kwarin gwiwa. Super Eagles na da fitattun ‘yanwasa da suka hada da Bictor Osimhen da Lookman da Chukwueze da sauransu.

Yanzu dai hankali zai koma kan koci, Eric Chelle ko zai iya lashe kofin. Akwai Kasashen Da Ba a Saka su a lissafi saboda raunin tawagoginsu

 

Kamaru

A kodayaushe ba tabbas a Kamaru, bayan rashin jituwa tsakanin shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Samuel Eto da Marc Brys. Sai dai kasar ta yi wasanni 12 ba tare da rashin nasara ba, kodayake ta yi tuntube a hannun tsibirin Cape Berde. Kamaru wadda ta lashe kofin sau biyar tana da gogewa a wasannin gasar.

 

Jamhuriyar Congo

Ita ma jamhuriyar Congo za ta yi fatan daukar fansa a hannun Senegal, wadda ta doke ta 3-2 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a badi. Ana sa ran tawagar wadda Yoane Wissa na Newcastle United da Fiston Mayele ke jan ragama, za ta so ta nunawa duniya cewar ba kanwar lasa ba ce.

 

Afirka ta Kudu

Bayan da Afirka ta Kudu ta taka rawar gani a wasannin da aka buga a 2023 da samun tikitin shiga gasar kofin duniya kai tsaye da za a yi a 2026. Afirka ta kudu na fatan nuna kwazo a wasannin da za ta fuskanta.

Kodayake yawancin ‘yan wasanta na buga wasa a gida daga Mamelodi Sundowns, duk da haka takan taka rawar gani da gagarar tawagogin da suke da fitattun ‘yan kwallon.

Za a buga gasar cin kofin Afirka a filaye tara cikin birane shida da suka hada da Rabat da Casablanca da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez. Birnin Rabat yana da manyan filaye hudu da suka hada da na Prince Moulay Abdellah Sports Compled, inda za a yi bikin bude gasar.

A Casablanca, filin Mohammed B da Wydad AC da Raja Casablanca ke wasanni, yana daga fitatcen filin da ake ji da shi a fadin kasar. Sauran biranen da za su karbi bakuncin wasannin sun hada da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez.

Jerin filayen da za a buga gasar

1 Prince Moulay Abdallah Sports Compled (Rabat)

2 Crown Prince Moulay El Hassan Sports Compled (Rabat)

3 El Barid Stadium (Rabat)

4 Olympic Anned Stadium of the Moulay Abdellah Compled (Rabat)

5 Mohammed B Stadium (Casablanca)

6 Fez Sports Compled (Fez)

7 Grand Stade de Tangier (Tangier)

8 Grand Stade de Marrakech (Marrakech)

9 Grand Stade d’Agadir (Agadir)

Me ya sa ‘Morocco ke kokarin mamaye kwallon kafar Afirka’a Getty

Kusan Shekaru 20 da suka wuce, Maroko ta rungumi wasanni, musamman kwallon kafa, ginshikin da tasirinta a Afirka da fiye da hakan. Ta hanyar karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka, tana da niyyar karfafa kimarta a matsayin kasa ta zamani mai kwanciyar hankali da kuma hangen nesa.

Nagartattun ababen more rayuwa na zamani ( filayen wasa da sufuri da otal-otal da dai sauransu) ba wai kawai alamar nasarar tattalin arziki ba da take da shi, tana kuma gudanar da mulki mai inganci da kishin nahiyar Afirka. Maroko na son gabatar da kanta a matsayin cibiyar kwallon kafa ta Afirka, mai iya shirya wani babban wasanni na kasa da kasa mai inganci.

Batun karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2025 a wuce wasanni.

Birnin Rabat, babban waje ne mai tasiri a harkokin diflomasiyya da kwallon kafa, ya zama abin tasiri da alfahari a duniya. Kasar ta riga ta zama hedkwatar kungiyoyin wasanni na Afirka da dama kuma ta ba da jari mai yawa a horo, ta hanyar Mohammed BI Academy ko kuma hadin gwiwa da wasu kungiyoyin Afirka.

Hadin gwiwar karbar gasar cin kofin duniya da za a yi a 2030 tare da Spain da Portugal babu shakka ya nuna yadda kasar ke da tasiri a gudanar da manyan wasannin kwallon kafa a duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
Wasanni

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
Wasanni

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara
Wasanni

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Next Post
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.