Furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa na jihar Nasarawa, Isah Umar ya zargi Jaruma Adama Saleh Pantami (Adaman Kamaye) da gudar masa da kudin aiki har naira 200,000 da ya umurce ta ta bai wa jaruma Zahra Diamond.
Da yake zantawa da manema labarai, Furodusan ya ce; bayan da aka ba ta kuɗin ta bai wa Zahra Diamond da nufin ta zo aikin wani fim mai suna ‘Takaddama’, ita wacce aka gayyata ba ta zo ba, ita kuma Adama ba ta mayar masa da kudin ba.
- Ban Taba Tunanin Fitowa A Cikin Fina-Finan Hausa Ba -Kamaye
- Maganar Da Na Taba Ji Da Ta Tsorata Ni A Kan Sana’ar Fim – Amina
Furodusan ya bayyana cewa ya ɓukaci lambar jaruma Zahra ne domin ta zo jihar Nasarawa wajen aikin fim ɗin, nan take Adaman ta ce ta santa kuma za ta kira ta.
Bayan sakar mata ragamar tattaunawa da jaruma Diamond, Adaman Kamaye ta ce sun shirya kan za a bata naira dubu 200, inda nan take ta umurci furodusan da ya ba ta kudin don ta tura mata.
Bayan Adaman ta kammala aikinta aka sallame ta tare da alkawarin cewa Zahra za ta zo gobe ko jibi amma shiru babu labari, daga bisani aka tuntubi Zahra Diamond inda ta bayyana cewa Adama ta kira ta a kan za ta yi aiki amma ta ce mata ba za ta iya zuwa ba saboda dalilai na tsaro.
Daga ƙarshe dai Furodusan ya zargi Adaman da cewa ta daina daukar wayarsa don jin inda kuɗinsa ya makale.
Labarin da ya janyo cece-kuce a masana’antar Fina-finan Hausa.
Sai dai kuma, da take mayar da martani kan zargin, Hajiya Adama Saleh Pantami, da ake wa laƙabi da Adaman Kamaye, ta ce; ita ba ta ci masa kudinsa ko kobo ba, hasali ma ya hada ta da lauyansa kuma sun warware komai da komai.
Da farko, ta ce ya gayyace ta aikin da aka ƙayyade za a yi a kwana huɗu ne, sai aka samu ƙarin kwana biyu a kai.
Bayan haka, Adama ta ce; na je da kayan saidawa kuma wanda ya gayyace ni aikin ya yi min ciniki na naira ₦285,000, da ya tashi biya sai aiko min da ₦240,000, ka ga saura ₦45,000.
A kashi na biyu kuma, ya yi min cinikin kaya na ₦257,000 sai ya ba ni ₦230,000, ya rage min ₦27,000. Sanan da ya buƙaci na kawo masa Zahra Diamond a matsayin jaruma da za ta yi aiki, ya bayar da ₦200,000 daga bisani Zahra Diamond ta ce ba za ta samu zuwa ba saboda gurin ya yi mata nisa.
“Dama kuɗin da ya ba ni na tura wa Zahra Diamond suna wajena ban tura mata ba. Sai na ce wa Salisu Mariri yaya batun ragowar kuɗin aikina da na kara kwanaki? Sai Mariri ya ce; kika san irin alherin da zai yi miki nan gaba? Sai na ce a’a aikin alheri daban na Sana’a daban. Duk abin da za a yi a yi da ƙa’ida. Ya ce; na yi haƙuri sai muka kamo hanya muka taho.”
To da ya nemi na dawo masa da kudin sai na ce ta yaya alhalin lissafin kuɗina (na sayayya) bai biya ni duka ba. Sai ya haɗa ni da wani Lauyansa a nan Kano muka yi magana, na yi wa lauyan bayanin ragowar kudin kayana da bai biya ni ba, sai lauyan ya ce na bar wannan zancen tun da lokacin da ya biya ban yi magana a kai ba, sai na ce to babu damuwa na bar zancen. Sai na ce to nawa za a biya ni kuɗin ƙarin kwana biyun aikin da na yi? Sai na ce ₦150,000, sai Lauyan ya ce; ya yi yawa, za a ba ki ₦100,000 sai ki mayar da ₦100,000. Na ce to babu damuwa, daga nan na tura wa Lauyan kudin ₦100,000. Wannan shi ne abin da ya faru.”