Adediji Moses, mahaifin ‘ya’ya uku da ya koka a shafukan sada zumunta kan zargin musanya yaron da aka haifa masa a asibitin koyarwa na Jami’ar Ladoke Akintola da ke Ogbomosho a Jihar Oyo, ya yi zargin cewa wasu mutum biyu sun yi garkuwa da shi bayan aika-aikar da aka masa.
Haka nan ya ce masu garkuwar sun yi masa barazanar cewa idan har bai janye karar da yake yi kan asibitin ba wani mugun abu zai iya faruwa da shi.
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Ayyukan Gina Cibiyoyin Masan’antu Da Gina Asibitin A Kauran Namoda
- Kamfani Ya Yaye Masu Kirkirar Fasaha 1,000 A 2023
Matashin mai shekaru 34 ya zargi asibitin koyarwa na LAUTECH da laifin musanya dansa lokacin haihuwa a watan Nuwamba 2018.
Adedeji a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The PUNCH ya koka kan barazanar da ake yi masa tun bayan da ya fito da labarin fili.
“Kwanan nan, na ziyarci wani gidan rediyo da ke Ibadan, Agidigbo FM, inda na kuma yi bayanin halin da nake ciki. Don haka, da safe na fitar da babur dina zan fara aiki sai na ga ga wasu mutum biyu kusa da gidana amma ba su yi kama da wadanda za su hau babur ba. Da na tashi daga aiki na dawo gida da yamma. Bayan na zauna a gida na dan wani lokaci, na so in je in ga wani, a lokacin da na dawo, sai na ga mutum biyu a gefen babur dina; akwai wata mota kirar Toyota Camry kofarta a bude a can gefe.
“Na ce da su don Allah su gyara ina so in dauki babur dina amma maimakon haka, sai suka tunkaro ni kamar suna son magana da ni da zuwa kusa da ni sai sika nuna min bindiga a gefena suka ce in shiga cikin motar. Na shiga mota sai suka sa wani kyalle suka rufe min fuska, don haka ban san inda aka kai ni ba. Sun yi tafiyar kusan mintuna 20 zuwa 30 kafin su tsaya. Daya daga cikinsu ya sauko ya yi waya suka fada min abubuwa da yawa.
“Suka ce aim un gaya maka idan baka dakatar da fallasa abin da ya faru da ‘yarka a sibitin LAUTECH ba to lamarin zai shafi mutane da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba. daga nan na fara rokonsu ina gaya musu cewa ba zan jawo wa kowa wani abu ya same shi ba amma ina son ’yata da matata su yi rayuwa mai kyau kuma a kula da su sosai. Sun sake yin magana da wani ta hanyar kiran a waya a karshe sun yanke shawarar za su sake ni. Sun gargade ni cewa suna kallona kuma idan na sake daukar wani mataki za mu gauraya da su. Bayan kamar misalin karfe 10 na dare, sai suka sake daukata suka mayar da ni Orita Nira inda suka dauke ni,” in ji Adedeji.
Ya kara da cewa, “Ni da matata ba mu da aikin yi kuma ina tukin Okada ne kawai don tsira. Idan sun taimake ni, zan iya kula da iyali ba tare da damuwa game da kula da lafiyar diyata ba. Iyayena sun bani kulawa kuma haka na tsira. Na yi imanin cewa ita ma za a iya kula da ita,” in ji shi.