Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai kawo muku yadda uwargida za ki hada miyar Tafasa:
Abincin Gargajiya
Tafasa, wani ganye ne da ake sarrafa shi domin yin amfani wajen yin miya.Ta fuskar kamanni, tafasa danyer shuka ce mai dauke da kananan ganye wadanda da kadan suka dara na Zogale. Ta fuskar tsawo kuwa, tsiron Tafasa bai wuce na Alayyafu tsawo ba. A duk lokacin da aka dafa ganyen tafasa, launinsa ya kan sauya daga kore zuwa baki.
Yadda ake miyar tafasa:
Daga cikin abubbuwan da ake tanada idan za a hada miyar tafasa sun hada da Albasa, Daddawa, Gishiri, Gyada, Kayan Yaji, Mai, Ruwa, Tafasa,Taruhu,Tattasai, Tumatur
Yadda za ki hada miyar Tafasa:
Da farko ki dora tafasa nama idan ki zuba gishiri da albasa ki daka kayan yajinki tare da daddawa ki zuba, sannan ki zuba kayan miyanki wanda dama kin gyara su ki kuma nika ko jajjagawa, sai ki zuba mai da magi idan za ki kara gishiri sai ki kara ki barshi ya ci gaba da tafasa, sai ki zuba gyadarki ki barta ta dahu, idan ta dahu sai ki wanke tafasar tare da dan gishiri ki zuba shikenan ki barta ta dahu.
Ita de miyar Tafasa ana yin ta kamar yadda ake miyar Zogale, za a daka gyada a saka tare da ganyen tafasar wanda ita ma za a wanke ta sosai tare da Gishiri. Da zarar ta dafu, to miyar tafasa ta samu kenan. Akan ci wannan miyar da kusan dukkanin nau’o’in tuwo.