Nasan kuna ganin wata alamar ‘mark’ na Good (√) mai dauke da kalar blue a gaban sunayen wasu da yawa daga cikin manyan mutane a Facebook ko manyan Pages na Facebook irin su BBC Hausa, Daily Nigerian da sauransu.
A mutane kuma akwai irinsu Rahama Abdulmajid, Sheriff Almuhajir da sauransu.
Kai tsaye kai ma za ka iya neman kamfanin na Facebook (META) da su saka maka wannan alamar a naka Account din ko Page kuma su saka maka kamar yadda suka saka wa wasu.
Ga yadda abin yake, da farko za ka je setting na Account dinka na Facebook, akwai wurin da za ka ga an rubuta ‘Help Center’ sai ka shiga wurin. Kana shiga zai bude maka, da zarar ya bude, daga can sama za ka ga akwatin yin tambaya, sai ka shiga wurin ka rubuta ‘How To berify My Profile Or Page’. Kana gama rubuta wannan, sai ka danna alamar searching, daga nan zai fara search.
Yana kammala search din, zai nuno maka da wani wuri da aka rubuta “You can fill out this form to verify your profile or page”. Idan ka lura da rubutun turancin za ka ga wurin da aka rubuta “fill out this form” an sanya mishi colour din Blue, sai kawai ka danna wurin, kana danna wa kai tsaye zai bayyanar maka da Form din da za ka cike domin mika musu bukatar ka ta sanya ma Account dinka Blue Badge.
Ka tabbatar ka tanadi hoton Passport dinka ko National ID Card ko Dribing license domin akwai wurin da za su bukaci ka saka wani Identification Document naka saboda tabbatar da Account din mallakinka ne. Farkon form din za su tambaye ka “Profile ko Page” ne kake so ka yi berifying din? Sai ka yi ticking din wanda kake so a yi maka berifying din. Kowane tsakanin Account da Page da akwai kalar Information din da suke bukata.
Akwai wani akwati da zaka gani wanda za ka saka Profile URL ko Page URL naka a wurin domin su binciki Account ko Page din naka don tabbatar da ya cancanci ayi berifying dinsa ko bai cancanta ba.
Bayan ka gama cike form din daga karshen form din akwai wurin da za ka yi Submitting, kana gama wa shikenan, za ka ga sun dawo da kai baya, alamun bukatarka ta tafi, dan haka za su yi bincike a kan Page din ko Account din naka zuwa wani lokaci da zaran sun kammala suka tabbatar babu wasu Restrictions a account din naka to za ka ga sun yi berifying account dinka. Idan kuma akwai wani Restrictions to lallai sai account dinka ya fita daga restrictions nasu sannan za su yi berifying dinsa.
Sannan idan ka yi Rekuesting sau daya ka ga an dade ba su turo maka wani sako ba kuma ba suyi berifying dinka ba, za ka iya kara cike form edactly kamar yadda ka cike a baya ka sake tura musu.