• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babbar Ganuwa Dake Jiayuguan Tana Taimakawa Ga Yayata Kyawawan Dabi’un Al’ummar Kasar Sin Jiayuguan, wuri ne dake yammacin lardin Gansu na kasar Sin, inda a ranar 20 ga watan Agustar shekara ta 2019, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar gani-da-ido, don kara fahimtar ayyukan kiyaye babbar ganuwar kasar mai dogon tarihi. Shugaba Xi ya jaddada cewa, da zarar an ambaci sunan kasar Sin, abin da mutum zai tuna ita ce babbar ganuwar kasar. A kan kuma tuna ta a duk lokacin da aka ambaci al’adun gargajiyar kasar Sin. Babbar ganuwar kasar Sin, da Koging Yangtze, da Rawayen Kogi, muhimman alamomi ne na al’ummun kasar, wadanda ke shaida nagartattun dabi’un mutanen kasar.

Jiayuguan, shi ne mafarin babbar ganuwar kasar Sin daga yammaci a lokacin daular Ming. A yayin rangadin da ya kai wajen, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya dace a gudanar da ayyukan raya al’adun dake tattare da babbar ganuwa da kara gadon su, da ci gaba da tallata nagartattun dabi’un al’ummar kasar Sin. Kuma a ‘yan shekarun nan, lardin Gansu na kara daukar matakai don bincike game da muhimman darajojin al’adun babbar ganuwa, da inganta ayyukan bayyana al’adun, tare kuma da kiyayewa gami da gudanar da ayyukan kirkire-kirkire a kansu.

  • Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa: Tarihi Daga Cibiyar Yinxu Ta Anyang Dake Kara Fahimtar Da Sirrin Wayewar Kan Sinawa

A halin yanzu, tsawon babbar ganuwa dake yankin Jiayuguan, ya zarce kilomita 43. A watan Agustan shekara ta 2019, shugaba Xi Jinping ya hau ganuwar dake wajen, inda ya ganewa idanunsa yadda aka tsara wajen, ya kuma jaddada cewa, babbar ganuwar kasar Sin na dauke da kyawawan dabi’un al’ummar kasar Sin, wato yin kokari ba tare da kasala ba, da zama tsintsiya madaurinki daya ba tare da yin kasa a gwiwa ba, tare kuma da nuna kishin kasa, abun da kawo yanzu ta riga ta zama muhimmiyar alama ta al’ummar kasar Sin gami da al’adunsu.

Yanzu haka, mutane suna bin sahun shugaba Xi na ziyartar babbar ganuwa dake yankin Jiayuguan, inda suke hawa matakala suna hangen tsawon ganuwar daga nesa, don kara fahimtar yadda babbar ganuwa ta ratsa manyan duwatsu, da sanin dogon tarihin dake tattare da ita.

He Shuangquan, manazarci ne dake aiki a cibiyar nazarin kayan tarihi dake lardin Gansu na kasar Sin, ya bayyana cewa: “Garin Jiayuguan gami da babbar ganuwar dake bayansa, ba ayyukan soja ne kawai ba, har ma suna kunshe da tarihin sama da shekaru 100, wadanda ke bayyana dabi’un al’umma. Wato sun nuna babban karfin al’ummar kasar Sin wajen kirkiro manyan abubuwa masu ban al’ajabi.”

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Sinawa
•Babbar ganuwa dake Jiayuguan

A wurin, an gina wani dakin adana kayan tarihi mai suna dakin adana kayan tarihi na babbar ganuwa ta Jiayuguan, dake zama irinsa na farko da ya nuna kayan tarihin dake kunshe da al’adun babbar ganuwa a kasar Sin. An gina shi ne bisa siffar babbar ganuwa, inda aka rataya wani babban zane mai fadin murabba’in mita 220, da ake kira “Babbar Ganuwa Mai Tsawo”, wanda ya bayyana kyan muhallin babbar ganuwa dake bangarorin gabas, da tsakiya, gami da yammacin kasar Sin. Haka kuma an baje kayan tarihi masu daraja sama da 2200 a ciki, wadanda ke bayyana dogon tarihin dake tattare da babbar ganuwar kasar, da nunawa al’umma yadda aka yi kokarin gina ta. Kamar yadda daya daga cikin masu ziyartar dakin ya ce, ya kara fahimtar dogon tarihi game da babbar ganuwar kasar Sin, da nagartattun dabi’un al’ummar kasar Sin, kuma yana alfahari da ganinsu.

Kiyaye babbar ganuwar kasar Sin, ba zai rasa nasaba da kokarin da ake yi na kiyaye kayan tarihin da aka gada daga kaka da kakanni ba, sa’annan ana kokarin yi musu kirkire-kirkire. A ranar 2 ga watan Yunin shekarar da muke ciki, shugaba Xi Jinping ya halarci taron karawa juna sani kan gado gami da raya al’adu a Beijing, inda ya jaddada cewa, ya kamata a dauki sabon nauyi a fannin raya al’adu, da takaita wasu sabbin ra’ayoyi da tunani da shawarwari da suka shafi al’adu da aka fitar, bayan da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira babban taronta karo na 18. Xi ya kuma ce, ya dace a himmatu wajen kiyaye al’adun gargajiya da kayan tarihin da muka gada daga kaka da kakanninmu, kamar yadda muke kokarin kare rayukanmu, domin kara tallata al’adun gargajiyar kasar Sin.

Sinawa
•Jiayuguan ya riga ya zama wani shahararren wurin yawon shakatawa a lardin Gansu

Bayan shekara da shekaru, babbar ganuwa ta gamu da matsalar lalacewa sakamakon wasu bala’u daga indallahi da suka wakana. A halin yanzu, ana kokarin amfani da wasu sabbin fasahohi domin kara sabunta babbar ganuwar kasar Sin. Har wa yau, sassan kula da kayan tarihi daban-daban na lardin Gansu, suna amfani da kananan jiragen sama marasa matuki, da sauran wasu na’urorin zamani domin tattaro bayanai kan babbar ganuwar gami da muhallin dake kewayenta, ta yadda za’a iya gudanar da aikin kiyaye ta ta hanyar da ta dace.

Xu Haijun, shi ne shugaban sashin sa ido kan al’adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni na cibiyar nazarin al’adu ta babbar ganuwar Jiayuguan. Ya bayyana ra’ayinsa cewa: “Kara kokarin kiyaye babbar ganuwar, da kara inganta ta, don al’adu su kara fadakar da mu, zai sa mu kara yarda da al’adunmu, da kara zage damtse a kokarin cimma burin kasar Sin.”

A ‘yan shekarun nan, ana kara gudanar da tarurruka iri-iri a dakin adana kayan tarihi na babbar ganuwar Jiayuguan, da gayyatar kwararru da masana kan harkokin babbar ganuwar don su ziyarci makarantu, da fadakar da dalibai kan ilmomi a wannan fanni. Sa’annan a wuraren yawon shakatawa dake garin Jiayuguan, an shirya wasu ayyuka masu ban sha’awa don yara da matasa, ciki har da “ina gyaran babbar ganuwa a Jiayuguan”, da “ina gyaran kayan tarihi a dakin adana kayan tarihi na babbar ganuwa”, da “ni ne mai gabatar da tarihin babbar ganuwa”, don dalibai su kara sanin tarihin yadda aka gina babbar ganuwar, gami da al’adun dake tattare da hakan. Daya daga cikin daliban makarantar firamare da suka halarci irin wannan aiki, ya bayyana cewa: “Ta hanyar halartar wadannan ayyuka, na karu sosai game da ilimin da ya shafi babbar ganuwar kasar Sin, da samun bayanai kan wasu jaruman da suka bayar da gudummawa a tarihi. Zan yi bakin kokarina wajen kiyaye babbar ganuwar, da bayyana labaranta yadda ya kamata.”

Tsohon garin Jiuyuguan, na da tsawon tarihi na daruruwan shekaru, inda aka samu musayar al’adun makiyaya da manoma tun lokacin baya, da shaida musayar al’adun kasar Sin da na kasashen yammacin duniya. A halin yanzu, mutane na jin dadin rayuwa a wannan wuri, inda suke kara nuna hazaka wajen kirkiro makoma mai haske.

A wurin yawon shakatawa dake garin Jiayuguan, ana gabatar da wani kasaitaccen wasan kwaikwayon gargajiya mai taken babbar ganuwa, wanda shi ne irinsa na farko da ya bayyana al’adun babbar ganuwa da labaran da suka shafi jarumai masu kare al’ummar kasar Sin daga harin kasashen waje, ko wadanda suka bayar da babbar gudummawa wajen shimfida “hanyar siliki” a tarihin kasar Sin, ciki har da Zhang Qian, da Huo Qubing, da Xuan Zang da sauransu, al’amarun da suka burge masu kallo kwarai da gaske.

A ‘yan shekarun nan, a tsohon garin Jiayuguan, ana kokarin hada wasu al’adu tare, ciki har da na babbar ganuwa, da na kan iyaka, da na hanyar siliki, don sanya sabbin abubuwa a cikin al’adun babbar ganuwa, da raya sana’ar yawon bude ido yadda ya kamata.

Sinawa
•Kallon Jiayuguan daga sama

A wajen taron karawa juna sani kan gado gami da raya al’adu da aka yi a ranar 2 ga watan Yunin shekarar da muke ciki a Beijing, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, al’adun kasar Sin na da hakuri sosai, wato suna kunshe da mabambantan abubuwa da yawa, al’amarin da ya kafa alkiblar musanyar al’ummun kasa, da aza tubali ga kasancewar addinai daban-daban a kasar.

Al’adun kasar Sin na da dogon tarihi, wadanda suka samu karfi da kuzari daga dabi’un al’ummar kasar, wato neman zama tsintsiya madaurinki daya. Kara musanya da yin koyi da juna, ya kara sanya sabbin abubuwa gami da wadatar da al’adun kasar Sin. Don haka, ya dace a ci gaba da tsayawa kan adalci, da yin koyi da musanyar ra’ayi tsakanin juna, da yin hakuri da juna, da kiyaye alamomin al’ummun kasar yadda ya kamata, da ci gaba da gadon al’adun gargajiya, ta yadda al’ummun kasar Sin za su samu bunkasa a duk fadin duniya.

Sinawa
Wani bangare na Babbar Ganuwa ta Jiayuguan

A nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta birnin Jiayuguan, Zhang Xun, ya bayyana cewa, Jiayuguan zai ci gaba da kiyaye al’adun da suka shafi babbar ganuwa, da kara koyon hikimomi daga al’adun gargajiya da aka gada zuriya bayan zuriya, da kuma sabuntawa gami da yin kirkire-kirkire ga al’adun gargajiya, a kokarin fadakar da al’umma game da tushe da muhimmancin al’adu. (Murtala Zhang)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sahihin Maganin Gyaran Fuska Ta Yi Kyau

Next Post

Birtaniya: An Yi Wa Malamar Jinya Daurin Rai Da Rai Bisa Laifin Kashe Jarirai

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

3 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

11 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

11 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

1 year ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Birtaniya: An Yi Wa Malamar Jinya Daurin Rai Da Rai Bisa Laifin Kashe Jarirai

Birtaniya: An Yi Wa Malamar Jinya Daurin Rai Da Rai Bisa Laifin Kashe Jarirai

LABARAI MASU NASABA

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

June 7, 2025
Neja

Dalilin Rashin Fara Aikin Kamfanin Takin Zamani Na Gwamnatin Jihar Neja

June 7, 2025
Adawa

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

June 7, 2025
2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

2027: Wasu Gwamnonin PDP Na Shan Matsin Lamba Don Sauya Sheka Zuwa APC

June 7, 2025
Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

Tsarin Jam’iyya Daya Ba Barazana Ba Ce Ga Tsarin Dimokuradiyyar Nijeriya – Gwamna Namadi

June 7, 2025
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

June 6, 2025
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

June 6, 2025
Daurarru

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

June 6, 2025
Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

June 6, 2025
Wutar lantarki

Fadar Shugaban Kasa Na Yunkurin Biyan Basukan Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 2

June 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.