“Ci gaban kowace kasa ko al’umma yana tafiya dogara ga ci gaban al’adunta a ko da yaushe, kuma cimma babban burin farfado da al’ummar Sinawa na dogaro da ci gaban al’adun kasar.”
A watan Nuwamban shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci Gidan Confucius da Kwalejin Nazarin Confucius dake birnin Qufu na lardin Shandong, domin kara fahimtar yadda ake jagorantar aikin gado da raya kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin.
- Fasahar Aikin Gona Da Ire-Iren Hatsi Masu Inganci Na Sin A Bikin Baje Kolin Uganda
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
Tun shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce, mai hikima Confucius ya ba da fifiko kan koyon ilmi, har ma ya zama abin koyi wanda ya cancanci a koya har abada. Ra’ayin da Confucius ya assasa, da akidun da ya bunkasa bisa wannan tunani, sun yi tasiri sosai ga wayewar kan kasar Sin.
A watan Satumba na shekarar 2014, a yayin bikin bude taron tattaunawa na kasa da kasa na tunawa da cika shekaru 2565 da haihuwar Confucius, da kuma babban taro na biyar na kungiyar akidun Confucius ta kasa da kasa, Xi Jinping ya nakalto layin farko na Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius dake cewa, “Abin farin ciki shi ne samun abokai daga nesa”, don maraba da mahalarta taron daga kasashe daban daban.
A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, akidun Confucius, da sauran akidu da al’adu da aka samar a lokacin kafuwar al’ummar kasar Sin, da ci gaban al’ummar kasar, sun zayyana yadda Sinawa ke gudanar da ayyuka a fannin ruhi, da tunaninsu da hankali, da nasarorin da suka cimma a fannin al’adu a fafutukar gina kasarsu tun zamanin da. Hakan na nuni da yadda al’ummar kasar Sin ke amfani da ruhi, kuma muhimmin abu ga al’ummar kasar wajen samun bunkasuwa.
Bisa la’akari da umurnin shugaban kasar, tsohon birnin Qufu ya kebe wuraren “Tsohon Confucius uku” wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a matsayin mafari, kuma ya kara da “Sabbin wuraren Confucius Uku” da suka hada da Kwalejin Nazarin Confucius, Gidan Tarihi na Confucius, da Nishan Mai Tsarki wato wurin da aka haifi Confucius, don inganta al’adun kasar Sin, da kara ilimantar da jama’a game da wannan falsafa a sabon zamani.
•Shiga “Wuraren Uku na Confucius” Don Kara Fahimtar Fadar Dake Tattare Da Al’adu Na Tsawon Shekaru Dubu
A lokacin bazara, birnin Qufu dake lardin Shandong yana jan hankalin masu yawon bude ido da yawa, Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da Kaburburan Confucius da Iyalansa masu kyau da haskakawa, sun kwashe dubban shekaru suna yada al’adun gargajiya na Confucius.
Tsohon rukunin gine-gine na Gidan Ibada na Confucius, wanda ke tsakiyar birnin Qufu daga arewa zuwa kudu, yana da ma’auni mai girma da tsayayyen tsari.
Daga bangaren gabashin Gidan Ibada na Confucius, akwai Gidan Confucius da aka sani da “Iyali na Farko a Duniya”, wanda ya kunshi gine-ginen da aka yi da shudin tubali da tayin mai launin toka.
Kabarin Confucius yana arewacin birnin Qufu, akwai duwatsun da aka sassaka kalmomi a kansu da yawa, hanyar zuwa wajen kabarin Confucius ta tsawon fiye da mita dubu daya.
A shekarar 1994, Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wuraren “Confucius Uku” wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.
“Idan kuna son kara fahimtar kasar Sin, ya kamata ku fara fahimtar Confucius, idan kuna son kara fahimtar Confucius, dole ne ku ziyarci ‘wurare uku na Confucius’.” Yang Chaoming, tsohon shugaban Kwalejin Nazarin Confucius, kuma fitaccen farfesa na kwalejin nazarin akidun Confucius na jami’ar Shandong, ya bayyana cewa, al’adun da Confucius ya kafa, wani muhimmin bangare ne na al’adun gargajiyar kasar Sin. Akidar da Confucius ya gabatar ta “kauna, aminci, ladabi, hikima, da mutunci” har yanzu su ne ruhin al’ummar Sinawa.
“Ya kamata a rika nuna gaskiya a lokacin da ake mu’amala da abokai”, “Idan ka hadu da mutumin kirki, to, kamata ya yi ka yi kokarin zama kamarsa, idan ka gamu da akasin haka, sai ka yi tunani ko kai ma kana da irin wannan rauni”…… Tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi Jinping ya dora muhimmanci sosai kan gadon al’adun kasar Sin, da dorewar wayewar kan Sinawa. Ya jaddada cewa, “Dole ne mu mai da hankali kan kare da gadon tarihi da al’adu, da kuma kare tushen ruhin al’ummar Sinawa.”
Ya sha ba da misali da wasu litattafan gargajiya na Confucius, ciki har da Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius a lokuta daban-daban, inda ya koyi hikima daga kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin wajen gudanar da mulkin kasa.
A yau, jama’a sun bi sahun Xi Jinping wajen ziyartar Gidan Confucius mai girman eka 240, lamarin dake kara nuna karfin al’adu.
Mataimakin daraktan kamfanin ba da hidimar yawon shakatawa ta al’adun Confucius na birnin Qufu mista Zhang Lei ya bayyana cewa, “Tun daga farkon wannan shekarar, yawan masu yawon bude ido da suka ziyarci wuraren shakatawa na ‘Confucius Uku’ ya karu sosai, inda ya kai miliyan 3.6, wanda hakan ya sa shi zama wurin binciken al’adun gargajiya mai muhimmanci.”
•Yadda Kyawawan Al’adu Ke Haskaka Makomar Raya Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin
Xi Jinping ya nuna cewa, “An haife mu a matsayin Sinawa, kuma muhimmin abu shi ne, muna da ruhin musamman na al’ummar Sinawa, da kuma dabi’un da jama’ar kasar ke amfani da su a yau da kullum da ba su sani ba. Muhimman dabi’un gurguzu da muke dabbakawa sun hada da gado da kuma daukaka kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin.”
Marigayi Confucius ya ce, “Idan mutane ba su da imani, ba su san abin da za su yi ba.”
Mutunci shi ne ginshikin daidaita rayuwar dan-Adam da gudanar da kasar.
A Cibiyar Ayyukan Wayewar Kai na Sabon Zamani ta Qufu, a ko wane karshen mako, malamin dake sassaka hatimi yana jagorantar yara don su ji fara’ar al’adan hatimi.
Zhang Guoqi, malamin dake koyar da fasahar sassaka hatimi a Gidan Sassaka na Qufu, ya ce: “Ana yada ruhin mutunci ne ta hanyar yin sassaka. Koyon fasahar sassaka ba wai kawai wani nau’i ne na raya al’adu ba, har ma yana cusa kyawawan al’adun gargajiyar Sinawa a zukatan yara.”
Al’amura sun canza, amma al’adun iyali ba su canja ba, a cikin Ka’idoji da Dokoki na Iyalin Confucius an rubuta cewa, “Ya kamata a koya wa zuriyar dake tafe ka’idoji da dokoki da aka gada daga kaka da kakanni, kuma a tabbata sun karanta tare da fahimtarsu bil hakki da gaskiya.”
Dukkan manyan sauye-sauye da suka faru a zamani ko a yanayin rayuwarmu, dole ne mu mai da hankali wajen gina iyali, wanda ya hada da ilimin iyali, da kuma tarbiyar iyali. Kong Minghui, malamin ilimin siyasa da tarbiya na Chongguangmen dake gidan Confucius, ya bayyana wa daliban dalla-dalla yanayin iyali da ilimin iyali na Confucius.
•Akidu Uku Na Confucius Sun Kawo Sabon Kuzari Ga Kyawawan Al’adun Gargajiya Na Kasar Sin
A kan hanyar zuwa kabarin Confucius, akwai Kwalejin Nazarin Confucius, wato daya daga cikin sabbin “Confucius Uku”. A shekarar 1996, Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ta amince da kafa Kwalejin Nazarin Confucius a matsayin hukumar musamman ta nazarin akidun Confucius.
A yayin binciken da ya gudanar a Qufu, Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata a martaba matsayin reshen falsafa dake nuna abubuwa a zahiri ne kadai suka fito daga halittu a yayin da ake nazarin Confucius da akidunsa, ta yadda za a yi amfani da abubuwan da suka gabata don zama darasi, da kawar da rashin gaskiya, da zurfafa nazari, ta yadda zai taka rawar gani a sabon zamanin da muke ciki.
A cikin ‘yan shekarun nan, Kwalejin Nazarin Confucius ya samar da jerin sakamakon bincike mai tasiri ga duniya. Musamman ma, aikin “Fassara Sin” da ya shafe shekaru 6 yana yi, wanda masana ilimin Confucius ke jagoranta.
A sa’i daya kuma, an fassara wasu littattafan game da Confucius da ke jawo hankalin Xi Jinping zuwa harsuna 16 da suka hada da Turanci da Jamusanci da yaren Koriya ta Kudu da dai sauransu, kuma sun karade kasashe fiye da 10 kamar Amurka, da Koriya ta Kudu, da Kyrgyzstan, kuma an buga fiye da kwafi dubu 500.
Amfani da ka’idodin magabata don bude sabuwar makomarmu. Wuraren “Confucius Uku” tsoffi da sabbi sun kunshi abubuwan da suka gabata da kuma nan gaba, kuma sun zama wata gadar dake haskaka da inganta yin kirkire-kirkire kan sauye-sauye da raya kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin.