Da alamu hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka, tana ci gaba da tsolewa wasu kasashe ido, wadanda a baya suke ta yunkurin kirkiro bayanai na karya da nufin bata wannan alaka mai dimbin tasiri da fa’ida ga bangarorin biyu. Amma bakin alkalami ya riga ya bushe.
Tun bayan kammala taron kolin BRICS kwanakin baya, masharhanta na ta tofa albarkacin bakinsu, game da tasirin kyakkyawan yanayin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, musamman ta la’akari da kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya furta, yayin taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afirka a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
- CMG Ta Kaddamar Da Wani Biki Don Fara Nuna Shirin “Journey Through Civilizations” A Kasar Peru
- Xi Ya Jaddada Gina Ingantattun Yankunan Cinikayya Maras Shinge Na Gwaji
A cikin kalaman shugaba Xi, ya bayyana bukatar dake akwai ta Sin da Afirka su yi hadin gwiwa, wajen sa kaimi ga tabbatar da odar kasa da kasa bisa adalci, da kiyaye yanayin duniya mai zaman lafiya da tsaro, da kuma raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga kowa.
Ko shakka babu, galibin masu sharhi sun gamsu da manufar kasar Sin, ta “A Gudu Tare A Tsira Tare”, inda suke bayar da misali da yadda hadin gwiwar sassan biyu ta samar da wani ginshiki, na gina muhimman ababen more rayuwa masu ingiza ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar nahiyar Afirka, matakin dake taimakawa matuka ga bunkasa masana’antu, da kyautata hada-hadar cinikayya a kasashen Afirka.
A zahiri take cewa, a baya bayan nan, kasar Sin ta wuce gaba a fannin yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, inda ba ya ga batun tattalin arziki da cinikayya, Sin na daukar kasashen nahiyar Afirka a matsayin abokan gina makoma, wadda ’yan baya za su ci gajiyarta.
Masu fashin baki na ganin cewa, yayin da alakar Sin da Afirka ke kara zurfafa, nan gaba sassan biyu za su karkata ga kulla hadin gwiwar raya fannin manyan fasahohi, irinsu kwaikwayon tunanin bil adama (AI), da binciken sararin samaniya, da sauran muhimman sassa da duniya ke mayar da hankali yanzu a kansu.
Fatan da dukkanin sassan nahiyar Afirka ke da shi a halin yanzu, shi ne dorewar kyakkyawar dangantaka mai armashi tsakaninsu da kasar Sin, ta yadda za su ci gaba da cin gajiya, da bunkasa kawancen gargajiya mai dadadden tarihi tsakaninsu da Sin.
Wani karin misali daga cikin irin fannonin da sassan biyu ke cin gajiya, shi ne tarukan karfafa zuba jari a wani mataki na taimakawa kasashen nahiyar raya bangaren masana’antun sarrafa amfanin gona da ma’adinai. Misali taron da aka gudanar a karkashin inuwar bikin baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Afirka (CAETE), a birnin na Changsha dake kasar Sin.
Bikin na bana dai ya shafi ayyuka masu alaka da gina kayayyakin more rayuwa da ba sa gurbata muhalli, da kiwon lafiya, da sarrafa amfanin gona, da gina yankunan masana’antu, da horar da matasa da ilimin sana’o’i, da sauransu. Kimanin kamfanoni 1500 daga kasashe 29 ne suka baje kayayyakinsu, adadin da ya karu da kaso 70 cikin 100 idan ka kwatanta da bikin da ya gabata. Haka kuma an kulla kwangiloli sama da 200 a yayin bikin, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 19.1.
Ban da haka, Najeriya kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, na daga cikin kasashen Afirka 8 da aka gayyata a matsayin muhimman baki a bikin na wannan karo, inda ta nuna wasu kayayyakin da ake samarwa a kasar, a wani wuri na musamman da aka kebe mata cikin dakin baje kolin kayayyaki.
Ministan kula da harkokin masana’antu da cinikayya na kasar Angola Victor Fernandes, ya ce kasashen Angola da Sin na da mu’amala mai karfi a fannin tattalin arziki da cinikayya, kuma akwai dimbin damarmakin hadin gwiwa a tsakaninsu.
Ministan ya ce, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta cimma kyawawan sakamako kuma zai kara fadada a nan gaba. Ya ce Sin da Angola sun dade suna hadin gwiwa, kuma tana maraba da karin ’yan kasuwar Sin da su zuba jari a Angola, musammam a fannonin masana’antu da aikin noma.
Shaidu sun kara tabbatar da yadda hadin gwiwar Afirka da Sin ke amfanar kasashen Afirka. Misali, yadda kasar Sin ta soke harajin da ake karba kan wasu kayayyakin da ake shigo da su cikin kasuwannin kasar Sin daga wasu kasashen dake nahiyar Afirka, da wasu managartan manufofin da Sin ta gabatar, kayayyakin kasashen Afirka masu tarin yawa, misali ganyen shayi na kasar Kenya, da ridi na kasar Habasha, da sauransu, sun fara shiga kasuwannin kasar Sin, lamarin da ya taimaka wa manoman wadannan kasashe samun karin kudin shiga.
Bayanai na nuna cewa, ko da a kasuwar Gaoqiao dake lardin Hunan na kasar Sin kadai, an shigar da waken gahawa da darajarsa ta kai dalar Amukra miliyan 10, cikin kasar Sin daga kasashen Afirka a shekarar 2022. Kana ana sa ran ganin wannan adadi ya ninka a bana.
Yanzu haka kuma, ababen hawa sun fara zirga-zirga a kan babbar gadar Cocody da kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CRBC ya gina, a Abidjan, babban birnin kasuwancin kasar Kwadibwa.
Shugaba Alassane Ouattara ya gode wa gudummawar da kamfanin na kasar Sin ya bayar, a fannin gina wannan babbar gada. Yana mai cewa, gadar za ta taimaka matuka wajen saukaka matsalar cunkoson ababen hawa a cikin birnin Abidjan, kuma aikin zai taka rawa wajen inganta rayuwar jama’a, kana abun alfahari ne ga jama’ar kasar.
A nasa bangaren, ministan kula da na’urori da kyautata hanyoyi na kasar Amedé Koffi Kouakou, cewa ya yi gadar Cocody muhimmiyar alama ce a birnin Abidjan, wadda ta samar da guraben ayyukan yi kimanin 3000 ga jama’ar birnin. Haka kuma kamfanin gine-gine na kasar Sin CITIC, ya mika sashen karshe na aikin ginin babbar hanyar mota da ta hade sassan larduna 17 dake kasar Aljeriya. Karkashin babban aikin ginin hanyar, CITIC ya kammala ginin kilomita 84 na hanyar.
Hanyar wadda ta hade sassan gabashi da yammacin kasar, ta dangana daga birnin Drean na lardin El Tarf a gabas mai nisa, zuwa birnin Raml Souk mai iyaka da kasar Tunisiya.
Ban da wannan kuma, wani shafin yanar gizo na sayar da kayayyaki mai taken Kilimall, da wani kamfanin kasar Sin ya kafa, yana samun karbuwa a nahiyar Afirka. Yanzu kamfanoni da daidaikun mutane fiye da 8000 na kasashen Afirka da na kasar Sin, sun bude kantuna fiye da 12000 a kan wannan shafin yanar gizo, inda ake sayar da wasu nau’ikan kayayyaki kimanin miliyan 1. Kana an ce a kasar Kenya kadai, wannan shafin yanar gizo ya taimaka wajen samar da karin guraben aikin yi fiye da 5000.
Bugu da kari, za a iya ganin karin nasarorin da aka cimma ta fuskar hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin a bangaren gina kayayyakin more rayuwa. Inda a kasar Najeriya, tashar jiragen ruwa ta Lekki da wani kamfanin kasar Sin ya gina za ta taimakawa birnin Legas wajen zama cibiyar jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa mafi girma a tsakiya da yammacin Afirka, kana za ta samar da sabbin guraben aikin yi kimanin dubu 200 cikin shekaru masu zuwa. Ga kuma layin dogo dake zirga-zirga a cikin birnin Lagos da kamfanin CCECC ya gina. A kasar Aljeriya kuma, wata tashar samar da wutar lantarki bisa zafin rana, tana samar da wutar lantarki a kai a kai ga wasu kauyukan da suke cikin hamadar Sahara. Sa’an nan a kasar Ghana, na’urorin zamani na sadarwa da aka sanya a yankunan karkarar kasar na samar da hidima ga manoman kasar fiye da miliyan 3.
Tambaya a nan ita ce, me ya sa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin Afirka da Sin ke sanya kasashen Afirka ci gaba? Amsar ita ce, shugabannin kasar Sin sun riga sun tabbatar da manufar kasar game da hadin gwiwa da kasashen Afirka, tun fiye da shekaru 20 da suka wuce, wato, kokarin zama aminiyar kasashen Afirka, da nuna musu sahihanci, da taimaka musu samun hakikanin ci gaba, gami da mai da adalci a gaban moriya yayin da take hadin gwiwa da kasashen Afirka. Kamar yadda babban jigon bikin CAETE na wannan karo ya nuna, wato “neman samun ci gaba tare, da more wata kyakkyawar makoma a nan gaba tare”, ya nuna cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana neman hadin gwiwa tare da kasashen Afirka don su ci gaba tare.
Shugaban kasar Malawi, Lazarus McCarthy Chakwera, ya bayyana a wata hirar da manema labarai cewa, zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Malawi da Sin za su taimaka wa Malawi wajen samun ci gaba mai ’yanci da dorewa, da bin hanyar raya kasa da ta dace da yanayin kasar.
Ya ce, bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da Afrika, a matsayin wani muhimmin dandali na zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, baje kolin ya bai wa sassan biyu damar kulla alaka tsakanin jama’a, da masana’antu, da gwamnatoci. Kasar Malawi ta halarci bikin ne a matsayin babbar bakuwa.
Shi ma kwararre a fannin tsara manufofi dan kasar Habasha, Farfesa Costantinos Berhutesfa Costantinos, ya ce hadin gwiwa da kasar Sin ya bunkasa ci gaban kasashen Afirka, yayin da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 3 ya kara ingiza saurin ci gaban da nahiyar ke samu.
A cewar shaihun malamin, yanzu haka, kasar Sin ce abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma, kuma kasa ta hudu a girman zuba jari a nahiyar. Har ila yau, alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2022, cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasashen nahiyar ta kai darajar dalar Amurka biliyan 282. Kuma cikin watanni hudu na farkon shekarar nan, adadin sabbin kudaden jarin kai tsaye da Sin ta zuba a kasashen Afirka, ya kai dala biliyan 1.38, adadin da ya karu da kaso 24 bisa 100 a duk shekara.
A daya bangaren kuma, tasirin Sin a fannin bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka, ya wuce batun samar da ababen more rayuwa, inda ya kutsa zuwa sauran muhimman fannonin samar da ci gaba. Gina yankunan raya tattalin arziki na musamman da Sin ta yi a kasashen nahiyar da dama, shi ma ya samar da karin damar bunkasa fannin masana’antun nahiyar Afirka.
Farfesa Costantinos ya kara da cewa, kasashen Afirka da kamfanoninsu, za su iya cin karin gajiya daga baje kolin, musamman a fannin bunkasa ayyukan masana’antu, ta yadda za su kara shiga kasuwannin Sin, da ma na sauran sassan duniya.
Kimanin shekaru 10 ke nan, tun bayan da shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya yi bayani game da manufar kasar Sin ga nahiyar Afrika a Tanzania, wadda ta tsara makomar huldar kasar Sin da Afrika a sabon zamani, wadda yanzu haka ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin bangarorin biyu.
Ita dai wannan manufa da shugaba Xi ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin, a shekarar 2013 ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna,
Bisa wadannan tsare-tsare, kasashen Sin da Afrika sun hada karfi da karfe, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, da nufin samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asiya da kuma nahiyar Afrika, wadanda yawan al’ummarsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al’ummar duniya baki daya. Bayan wadannan shekaru, ana iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a fannoni da suka hada da tattalin arziki, ilimi, da cinikayya, da kayayyakin more rayuwa, da al’adu, da noma, da raya masana’antu da ma kaiwa juna ziyara a bangare manyan jami’ai gami da shugabanni. Tarukan dandalin hadin gwiwar kasar Sin da nahiyar Afrika FOCAC, da suka gudana a lokuta da wurare daban-daban, gagarumin ci gaba ne ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Wadanda ke aikewa da muhimmin sako ga al’ummomin duniya cewa, Sin da Afrika sun hada hannu don samun nasara tare. (Ibrahim Yaya)