Masanin harkar aljanu da ruhainai kuma tsohon mataimakin kwamadan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dakta Maigida Kachako ya bayyana cewa har da aljanu sun shiga zanga-zangar kuncin rayuwa da ya gudana a Jihar Kano.
Masanin harkar aljanun ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai Jihar Kano a wanan makon.
- Firaministan Pakistan: Bunkasuwar Sin Ya Zama Abin Misali Ga Kasar
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Ayyukan Yi Miliyan Ɗaya – Ɗan’agundi
Dakta Kachako ya ce su ma aljanu matsin rayuwar ta shafe su, domin daga cikin manyan abincin aljajanu akwai kashin da mutane suka yi tsotsa suka yar, wanda shi ma kashin ya yi karanci sakamakon matsin rayuwa a Nijeriya, inda hakan ya tillasta wa aljanu shiga sahun mutane wajen gudanar da zanga-zangar a Jihar Kano.
Ko da aka tambayi Dr Kachako, ta wacce hanya ya yi magana da aljanun har ya san za su shiga zanga-zangar, ya ce, sun yi magana da aljanin da ya fada masa hakan ne yayin da yake wa wata mara lafiya rukiya inda aljanin ya tabbatar masa da cewa su ma za su shiga zanga-zangar.
“Kuma tun da na yi rukiyar aljanin ya fita ya bar ta, ka ga ba sai na dawo da shi ba don ya ba ni labarin yadda suka shiga zanga-zangar. Ni ba labarin shigarsu zanga-zangar ya dame ni ba illa samun lafiyar wanda na yi wa rukiyar. Amma dai (aljanin) ya gaya mun cewa za su shiga zanga-zangar kuma na ce masa to su ji tsoron Allah.
“Lokacin da nake tambayarsa me ya sa ya shiga jikinta ya sa mata ciwon kai da sauransu, sai ya ce shi yanzu ma zai bar jikinta domin za su je su shiga zanga-zangar. Na ce masa kun shirya? Ya ce e, na ce kuna da yawa? Ya ce e, sai na ce masa to muna muku nasiha ku ji tsoron Allah, ka ji yadda abin yake.”
Har ila yau, Dr Kachako ya kara da cewa, bisa yadda zanga-zangar ta kasance da cincirindon jama’a da yadda akayi ta’adi na rashin hankali ya nuna akwai nau’in aljanu daban-daban da su ka shiga cikinta. Yana mai bayyana cewa duk wanda ya san tarihin Musulunci ya san aljanu sun shiga yaki na taimakon addini a zamanin magabata.