A kauyen Gulu, mazauna kauyen suna tattaunawa kan bukatunsu, inda malam Shen Shaohua ya ce, “Akwai mutane 6 a gidana, shi ya sa muna bukatar sassan da abin ya shafa su kara inganta manufar inshorar lafiyar mazauna kauyuka.” malam Zheng Wangchun mai shekaru 37 a duniya, ya kuma rubuta bukatun Shen da na sauran mazauna kauyen bi da bi.
Kauyen Gulu kauye ne na ‘yan kabilar Yi, wanda ke can karkarar lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, kuma malam Zheng Wangchun haifaffen kauyen ne, wanda a shekarar 2023, aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. Tun lokacin kuma, kullum ya kan tattauna da magidanta fiye da 200 na kauyen.
Bayan tattaunawa da ya yi da mazauna kauyen, Zheng ya fahimci cewa, yawan kudin da aka biya ya karu a kowace shekara duba da kyautatuwar tsarin inshorar lafiya na Sin, sai dai ba abu mai sauki ba ne ga mazauna kauyen kamar Shen Shaohua mai mambobin iyali da yawa su biya kudaden. Amma idan ba su shiga inshorar ba, ya yiwu su koma talauci idan rashin lafiya mai tsanani ya same su. Hakan ya sa a taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar Sin da ke gudana a kwanakin nan a birnin Beijing, Zheng ya hallara tare da gabatar da shirin da ya shafi rage yawan kudaden da jama’a za su biya kan inshorar lafiya, da habaka amfanin inshorar ga karin mutane.
Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, sassan majalisar gudanarwar kasar Sin sun daidaita irin shirye-shiryen 8783 kan lokaci a bara, wanda ya kai kashi 95.1% da dukkanin shirye-shiryen da ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar suka gabatar. Wadannan shirye-shirye masu dauke da burin jama’a kamar na mazauna kauyen Gulu, wata muhimmiyar hanya ce ta tattara ra’ayi da basirar jama’a.
A nan kasar Sin, yawan ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin irinsa Zheng Wangchun ya kai kusan 3000, wadanda suka fito daga wurare, kabilu ko sana’o’i daban-daban, wadanda kuma suka kasance mahada dake sada tsakanin jama’a da gwamnatin. Matsayinsu na tabbatar da ana jin muryoyin jama’a duk inda suka fito. Wannan shi ne tsarin majalisar wakilan jama’ar Sin, hanyar da jama’ar kasar ke sa hannu cikin harkokin kasar don tabbatar da hakkin jama’a a cikin zaman rayuwarsu a bangaren demokuradiyya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp