Daga dukkan alamu manyan arewa daga bangarorin rayuwa daban-daban, tun daga ‘yan siyasa jami’an tsaro, tsofaffin shugabanni, sarakuna da sauran masu fada a ji a yankin arewacin Nijeriya sun tabbatar da bukatar hada kai don yi wa lamarin matsalar tsaro da ta addabi sassan arewacin kasar nan taron dangi, ‘A Yi ta ta Kare’.
Wannan kudurin ya fito fili a taron da gamayyar kungiyoyin yankin rewacin ‘Coalition Of Northern Groups’(CNG) ta gabatar a Abuja ranar Labara 24 ga watan Janairu 2024.
- AFCON 2023: An Fitar Da Jadawalin Zagaye Na 16
- An Maido Da Huldar Diplomasyiya Tsakanin Sin Da Nauru, CMG Ta Bude Ofishinta A Nauru
A jawabinsa, shugaban taron kuma tsohon shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa, in har ana saon cin galabar matsalar tsaron da ke addabar yankin arewa dole a fuskanci lamarin ta haryar taron dangi tare da amfani da dabaru da dama da suka hada da karfafa jami’an tsaronmu da inganta hanyoyoyin tattara bayanan sirri tsakanin jami’anm tsaro. Haka kuma zuba jari don bukasa bangaren ilimi da tattalin arziki tare da tsunduma sarakuna cikin tafiyar da kasa zai yi mana maganin matsalar tsaro daga tushe.
Ya kuma nemi a tabbatar da hadin kai a tsakanin rundunonin tsaro don su yi aiki tare, “Dole gwamanatocin jihoji da na tarayya su hada kai a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda da masu garkwua da mutane, hadin kan su tare da tafiya tare shi ne zai tabbatar da nasarar da ake bukata a wannan tafiyar’’ in ji shi.
A nasa jawabin tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya dora laifin matsalar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu a sassan Nijeriya a kan yadda aka siyasantar da lamarin tsaro, “Dole mu fuskanci harkar tsaro ba tare da la’akari siyasa ba in har muna son tabbatar da kare rayuwa da dukiyoyin al’ummar Nijeriya a wannna lokacin’’, in ji shi.
Ya kuma bukaci a yi amfani da dabaru da dama wajen yaki da ta’addanci, “Ka da mu bayar da muhimmanci kawai ga amfani da karfi a yaki da muke yi da matsalar tsaro, ya kamata a yi amfani da dabarun rungumar ‘yan ta’addan da samar musu wasu bababen more rayuwa, domin yaki kawai ba zai kai mu ga samun tabbataccen zaman lafiya ba a Nijeriya.
Haka kuma taron ya samu halatar mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad, inda a jawabinsa ya bayyana cewa, Sarakuna a fadin tarayyar Nijeriya a shirye suke don tafiya tare da dukkan wani yunkuri na samar da zaman lafiya a sassan Nijeriya musamman arewacin Nijeriya. Ya yi alkawarin mika sakamakon matsayar da aka cimma a taron ga taron kungiyar sarakuna arewa da za a yi a watan Faibrairu don a tattauna tare da daukar matakin da ya kamata.
Ya ce, Sarakuna na da gudummawar da za su bayar kuma za su ci gaba da bayarwa wajen tabbatar da tsaron al’umma a arewa. Ya kuma yaba wa gamayyar kungiyoyin arewa a kan shiryan taron.
A nata tsokacin, Kungiyar Dattawan Arewa, a karkashin shugabancin Farfeasa Ango Abdullahi, ta nuna jin dadinta tare da yaba wa gamayyar kungiyoyin yankin arewa da suka samu shirya wannan taron da ya zama irinsa na farko a tarihin yankin arewa.
Jawabin haka ya fito ne daga bakin mai magana da yawun kungiyar, Kwamrade Abdul-Azees Suleiman, wanda ya ce, taron da ya hada masana daga bangarori da dama zai samar da mafita da mahukunta za su yi amfani da ita wajen samar wa yankin arewa maganin matsalar tsaron da ake fuskanta wanda ta haifar da nakasu ga tattalin arzikin kasa ya kuma ci rayukan al’umma da dama a ‘yan skekarun nan.
Ya kuma ce, taron ya samar da dandamalin da masana za su baje kolinsu a kan yadda za a kawo karshen mastalar tsaro a kasar na, a kan haka ya bukacu hukumomin gwamnatocin jihohi da na tarayya su rungumi matsayar da taron ya fitar don yin aiki da su, ta haka za a tabbatar da nasarar da ake bukata.
Da yake jawabin godiya ga maharta taron, daya daga cikin jagororin da suka shirya taron, Dakta Nastura Ashir Shariff ya bayyana yadda matsalar tsaro ta shafi dukkan bangaren rayuwar al’ummar Nijeriya musamman yankin arewa.
Ya kuma amince da shawarar cewa, yaki da mastalar tsaro na bukatar hadin kan dukkan bangarorin al’umma da kuma aiki tare a tsakanin gwamnatin jihohi da na tarayya har zuwa matakin kananan hukumomi,. Ya nemi hadin kai da kasashe makwabta domin ta haka za a iya dakile rikice-rikicen da ke tsallakowa daga waje zuwa cikin gida Nijeriya.
Nastura Ashir Shariff ya kuma nemi gwamnati ta kara kaimi wajen yaki da talauci da tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta, ya ce, matsalar rashin aiki yi a tsakanin matasa yana taimakawa wajen yaudarar matasanmu su fada ayyukan ta’addanci.
Daga karshe ya nemi gwammati ta yi amfani da dukkan sakamakon da taron ya fitar don kawo karshen matsalar tsaro a yankin arewa. Taron ya samu halarta gwamnoni, sarakuna gargajiya, masana harkokin tsaro da sauransu.