Dogaron ba bankuna Nijeriya ke yi wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) a wajen gudanar da harkokinsu yana ta kara karuwa yayin da bayani ya nuna cewa, bankunan Nijeriya sun wawuri bashin fiye da Naira Tiriliyan 3.03 a watan Satumba alhali a watan Agusta bashin Naira biliyan 323.97 suka karba, wanda hakan ke nuna an samu karuwar kashi 835 na bashin da suka ci daga watan Agusta.
Haka kuma bayani ya nuna cewa, babban bankin ya zuba jarin fiye naira Tiriliyan 10 a bangarorin tattalin kasa daban-daban amma kuma babu wani abin a zo a gani, don kudaden da aka zuba basu nuna wani gaggarumin bunkasar tattalin arzikin kasar ba.
- Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke
- Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a
Bayanai daga shafin intanet na Babban Bankin ya nuna cewa, tun daga farkon watan Satumba har zuwa ranar Juma’a 22 ga watan basussukan kudi da bankuna kasuwancin kasar nan suka karba ya kai Naira Tiriliyan 3.028, amma a watan Agusta bankuna sun karbi bashin naira Biliyan 323.97, wannan ya sa masana ke bayanin cewa, lallai dogaron da bankuna kasuwanci ke yi wa Babban Bankin kasa ya yi yawa, kuma hakan ba zai harfar wa tattalin arzikin kaasa da mai ido ba.
Bankuna sun karbi kudaden ne ta hanyar tsarin bayar da bashi na CBN mai suna “Standing Lending Facility (SLF)” wanda tsari ne ta yadda bankuna za su iya karbar kudade don biyan bukatun su na kusa da kuma na nesa, musamman yayin da abokan huddarsu suka bukaci karbar kudi masu yawa a lokaci daya.
Amfani da tsari na SLF na nuna cewa, Banki na fuskantar tsananin bukatar kudi ko kuma yana jin jiki sakamakon tsare-tsaren Babban Banki ko kuma yana fuskanta wasu basussuka da ya kasa karbar daga abokan hulda’
A cikin shekaru biyu da suka wuce, CBN ya bullo da wasu tsare-tsare da suka tilastawa bankuna shiga matsalar rashin tsabar kudi wanda hakan ya haifar da bukatar su nemi kudi a kusan duk mako don abokan huldar su, ana kuma tunanin wannan na daga cikin dalilin da haifar da yawan bashin da bankunan suke ci.
Haka kuma wasu mambobin kwamitin kula da yadda CBN ke sarrafa kudade sun bayyana cewa, tsarin Babban Bankin yana da alfanu ga tattalin arzikin kasa kuma Baban Bankiin na a kan tsarin da gwamnati ta dora shi, sun kuma yaba da yadda bankuna ke gudanar da harkokinsu. Wani mamba a kwamitin mai suna Adenikinju Festus, ya ce, bankuna sun yi kokari amma lallai ya kamata su kara kaimi, amma lallai ya kamata a yaba musu don bayani ya nuna cewa, harkokinsu ya karu daga kashi 11.2 a watan Yuni na shekarar 2023 zuwa 13 a watan Mayu na shekarar Mayu 2023. Ya kuma nemi su bude wasu hanyoyin samun kudade su rage dogaro da babban Banki, ta haka tattalin arzikin kasar zai bunkasa.