Barcelona ta doke Bayern Munich a gasar cin zakarun Turai da suka buga da ci 4-1 a daren Laraba, a wani bangare na ramuwar gayya a kan gwarazan Jamus.
Raphinha ne gwarzon dan wasan Barcelona a wannan wasan, inda kyaftin din ya jefa kwallo uku rigis a ragar Manuel Neuer a wasa na 100 da ya buga wa Barcelona tun bayan zuwansa daga Leeds United ta kasar Ingila.
- Tsarin BRICS Na Samun Karin Karbuwar Kasashe Daban-Daban
- Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano
Matasan ‘yan wasan tsakiyar Barcelona Marc Casado, Pedri da Fermin Lopez sun matukar yin kokari a wasan inda suka hana manyan ‘yan wasan Bayern Munich sakat da suka hada da Joshua Kimmich Michael Oliseh da Thomas Muller.
Wannan nasara da Barcelona ta samu ita ce ta farko a cikin wasanni shida na baya-bayan nan da kungiyoyin biyu su ka hadu a tsakaninsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp