• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ci Gaban Kasar Sin Ke Tasiri A Duniya

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Idan muka ce duniya baki daya ta bibiyi sanarwar cikakken zaman taro karo na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20 ba mu yi karya ba. Magoya baya da abokan huldar Sin sun kasa kunne su ji tabbacin labarin kwanciyar hankali da daidaiton tsarin ci gaban kasar, yayin da masu sukar lamirin kasar suka yi ta kokarin gano alamun karuwar matsaloli, da damuwa, ko ma yiwuwar rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin JKS. A karshe dai, magoya baya sun samu dalilan da suka kwantar musu da hankali, kuma masu zagi dole ne su kasance cikin takaici. A bayyane, zaman ya nuna ci gaba a tsarin siyasa, da tattalin arziki da zamantakewa da aka tsara a babban taron JKS karo na 20 da aka gudanar a shekarar 2022. Zaman ya mayar da hankali ne kan al’amuran cikin gida da nufin kammala aikin zamanantarwa bisa tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da gina ingantacciyar hanyar tattalin arziki ta gurguzu da kuma zamanantar da tsarin kasar da iya tafiyar da harkokin mulki.

Mu dubi tsarin kasuwancin duniya na wannan zamani, jimillar kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya kai kusan dalar Amurka tiriliyan 6, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ga kasashe fiye da 120. Kasar Sin tana da fiye da rabin sabbin motocin lantarki da aka sayar a duk duniya a yau, kuma tana daukar sama da kashi 80 cikin 100 na kayayyakin samar da wutar lantarki bisa hasken rana a duniya. Yana da wuya a yi tunanin kasuwannin duniya na kwamfutoci da na’urorin laturoni, da sinadarai na hada magunguna, da injuna, da motoci, da sauran kayayyaki daban-daban ba tare da tabo rawar da kasar Sin ta taka ba.

Kusan shekaru 100 da suka shige, tsohon shugaban Amurka Franklin D. Roosevelt ya bayyana cewa, “Yadda matsayinmu a tarihi ke cike da haske haka yake da hadari. Ko dai duniya ta karkata zuwa ga ci gaba da hadin kai da wadatar arziki a ko’ina, ko kuma ta rarrabu.” Wannan gaskiya ne a shekarun 1930s kuma ba shakka haka lamarin yake a zamaninmu na yau. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne wajen samun nasarar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin saboda hakan na da matukar tasiri ga tattalin arzikin duniya. Kuma wadanda ke yi wa Sin munanan fata harbin kansu kawai suke yi a kafa. (Mohammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
Sojoji Sun Ceto Wata Ƴar Chibok, Sun Miƙa Ta Ga Gwamnatin Borno

Sojoji Sun Ceto Wata Ƴar Chibok, Sun Miƙa Ta Ga Gwamnatin Borno

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.