A jiya Laraba, mahukuntan Kwastam sun bayyana cewa, hada-hadar shige da ficen kayayyaki da aka yi tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Macao, sun kai na yuan biliyan 471.43, watau kimanin dala biliyan 65.58, daga Janairun shekarar 2000 zuwa Nuwamban 2024.
Cikin shekaru fiye da 25 da dawowar Macao karkashin kasarsa ta asali, hada-hadar kasuwancin da ake yi tsakaninsa da babban yankin kasar Sin a shekara, sun karu daga yuan biliyan 4.87 a shekarar 1999 zuwa yuan biliyan 27.01 a shekarar 2023, wanda yake nuna ana samun matsakaicin karuwar abun da kashi 7.4 cikin dari a ko wace shekara, kamar yadda mahukuntan Kwastam na Gongbei a yankin Zhuhai, daya ga cikin biranen lardin Guangdong na kasar Sin mai iyaka da Macao suka bayyana.
A cikin watanni 11 daga farkon shekarar nan kuma, cinikayya sun karu a tsakanin bangarorin biyu da kashi 9.7 cikin dari, a mizanin shekara-shekara zuwa yuan biliyan 25.94.
A fiye da shekaru 25 da suka gabata, kasuwannin yankin musamman na Macao suna kara jawo hankalin kamfanoni masu zaman kansu na babban yankin kasar, inda hada-hadar kayayyakin da suke shige da ficensu ke karuwa da yawa kamar yadda bayanan mahukuntan suka nunar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)