Daruruwan dubban jama’a ne suka yi dafifi a Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi domin halartar Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 37 wanda har ila yau yake nuna cika shekara 137 da haihuwarsa a duniya.
Tun a makon da ya gabata garin Birnin Kebbi ya dauki baki daga Kasashen Afirka ta yamma da kuma mutane daga jihohin Nijeriya da suka yi tattakin zuwa jihar domin halartar taron bikin Mauludin na Sheikh Ibrahim Inyass. Inda hanyoyin mota da gidanjen saukar da baki na babban birnin jihar ya cika makik da mutanen da suka shigo taron Mauludin.
Hatta ‘yan kasuwa na waje da na cikin gida Nijeriya ba a bar su a baya ba, domin sun kasa kayyayaki iri daban- daban don sayarwa. Babban taron Mauludin ya gudana ne a filin sukuwa da ke babban birnin jihar.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin karbar bakoncin maulidin a Jihar Kebbi, Khalifa Yahaya Bawa Jega ya bayyana jindadinsa ga irin yadda jama’ar Kasashen Afirka da na gida Nijeriya suka yi tattakin zuwa jihar kebbi don gudanar da taron bikin Mauludin na Sheikh Ibrahim Inyass a babban birnin jihar wanda ya ce wannan ba karimain karamci ba ne.
Ya ce” Muna godiya a madadin ‘yan darikar Tijjaniya na jihar Kebbi. Muna kuma addu’a Allah ya maida kowa gidansa lafiya mun gode.”
Haka zalika ya gode wa gwamnatin jihar da mutanenta kan goyon baya da gudunmuwar da suke bai wa Tijjaniya a jihar.
A nashi É“angaren, Khalifan Tijjaniyya Nijeriya, Muhammad Sanusi na biyu kuma Sarkin Kano na 14, ya bayyana cewa” makasudin gudanar da toron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass shi ne don tunawa da ranar haihuwar Babban Shehin, da kuma bayyana irin ayyukan da ya gudanar na yada addini da irin fatawa da kuma sauran ayyukan alhairi da ya assasa a cikin duniya. Saboda haka ina kira ga jama’ar mu da muyi koyi da Sheikh Ibrahim Inyass.”
Haka zalika, ya yi kira ga jama’ar musulmi da cewa nan da mako daya mai zuwa za a gudanar da zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattijai saboda irin muhimmanci da ke tattare ga zaben, jama’a ka da su yi kasa a guiwa su tabbatar da sun fito don zaben Shugaban kasa da ‘yan majalisar dattijai da suka dace.
Har ila yau, ya jaddada cewa “akidarmu ita ce yawaita salati da gudanar da zikiri da kuma gode wa Allah. Mu dauki dabi’a hakuri da wanzar da zaman lafiya da kuma yawan bauta wa Allah.
“Nijeriya na bukatar addu’o’i domin kara samun zaman lafiya mai dorewa da samun kwanciyar hankali ga ‘yan kasa. Mu kuma yi addu’a Allah ya sa a yi zabe lafiya a gama lafiya.”
Da yake jawabi tun da farko, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass, Shehu Mahi Ibrahim Inyass ya bayyana jindadinsa da kuma yaba wa mutanen Nijeriya musamman jihar Kebbi inda aka gudanar da taron bikin Mauludin, bisa mutuntawa da ake yi wa Sheikh Ibrahim Inyass da kuma ci gaba da aiwatar da ayyukan da ya yi wa addini.
“Ina godiya a madadin diya da jikoki na gidan Shehu Ibrahim Inyass kan irin soyayar da ake nunawa . Mun gode mun gode.”
Shi kuwa Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yi godiya ga shugabanni kungiyar bisa karamcim da aka yi wa jihar na ba ta damar karbar bakoncin taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass.
“Jihar Kebbi gidan darikar Tijjaniya ne don haka gwamnatin jihar ba za ta yi mamaki ba don an zabe ta a matsayin wajen da za a gudanar da taron bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass na Kasashen Afirka.
A cewarsa, gwamnatin jihar Kebbi za ta ci gaba da ba da goyon baya da gudunmuwarta ga ‘yan darikar don kara samun ci gaban addini da kuma al’ummar mu da kara samun zaman lafiya da tsaro ga jahohin kasar Nijeriya baki daya.
“Bisa ga wannan karancin muna kara godiya ga shugabanni da khalifan Sheikh Ibrahim Inyass da na kasar Nijeriya da sauran duk wadanda suka taimaka aka samu nasarar gudanar da taron bikin.
Daga karshe Gwamnan ya bayyana sakon fatar Alhairi na dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shatima da Ministan shari’a Abubakar Malami da kuma ba da hakuri ga rashin halartarsu a wajen bikin taron, yana mai cewa” saboda yanayin hazo jirgin su bai iya tasowa ba, wannan shi ne ya hana su halartar bikin. Bisa ga hakan a madadinsu ina mai baku hakuri. Muna godiya kwarai da gaske Allah ya maida kowa gidansa lafiya.”
Haka kuma Gwamna Bagudu ya kara yin game da zaben da ke tafe, yana mai cewar, “Ina kara tunatar da jama’a su fito ranar 25 ga watan 2 na shekara ta 2023 don zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dattijai sobada muhimmancinsa ga duk ‘yan kasar Nijeriya.
Maulidin na Sheikh Ibrahim Inyass dai ana gudanar da shi ne duk shekara inda ake karbar bakuncinsa a jihohin Nijeriya.