A shekarar 2016 ce, James Blahos ya samu wani mummunan labarin cewar an gano mahaifinsa na fama da cutar sankara, wadda ta riga ta yi muni.
James, wanda ke zaune a garin Oakland, a Jihar California na kasar Amurka ya ce, “Ina matukar son mahaifina, ga shi zan rasa shi.” Ya sha alwashin amfani da sauran lokacin da ya rage wa mahaifin nasa na rayuwa yadda ya kamata.
- ‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu
- Li Qiang Ya Yi Kira Ga Sin Da Equatorial Guinea Da Su Kare Moriyar Bai Daya Ta Kasashe Masu Tasowa
“Na zauna tare da shi, inda ya ba ni tarihin rayuwarsa, na kwashe sa’o’i ina nadar tarihinsa da yake ba ni da kansa.”
Lamarin ya zo daidai lokacin da James ke kokarin shiga harkar ci gaban zamani ta kirkirarriyar basira (AI) daga nan ne ya fara aikinsa.
“Sai na yi tunanin me zai hana na yi wani abu da wannan lokaci da na samu?. Domin na samu abun da zan rika tunawa da shi da kuma jin tamkar yana tare da ni.”
Mahaifin James ya rasu a shekarar 2017, dab da lokacin da James din ya samar da manhajar kirkirarriyar basira wadda ke amsa tambayoyi kan rayuwar mahaifin nasa cikin muryarsa.
Masana kimiyya sun dade su na hasashen yadda za a iya ci gaba da amfani da wasu abubuwa na mutanen da suka mutu, to a yanzu ci gaban harkar fasasha ya sa mafarkin nasu ya zama gaskiya.
A 2019, James ya mayar da abin da ya kirkira zuwa wata manhaja wadda ya rada wa suna ‘HereafterAI’, wato kirkirarriyar basirar bayan mutuwa, wadda ke bai wa duk mai bukata damar nada tare da amfani da muryar ‘yan’uwansu ko bayan sun mutu, kamar yadda BBC ta nakalto.
Ya ce duk da cewa manhajar ba za ta cire masa damuwar rashin mahaifinsa ba, amma ta samar masa abun da ba zai iya samu ba in da bai yi hakan ba.
Yayin da manhajar ‘HereafterAI’ ke bai wa masu amfani da ita damar sanya hoton ‘yan’uwansu da suke so su fito a kan waya ko kwamfuta a lokacin da suke amfani da manhajar, wani kamfanin kirkirarriyar basirar ya kara inganta lamarin.
Wani kamfanin sadarwar zamani da kirkirarriyar basira a Koriya ta Kudu mai suna DeepBrain AI, yana samar da kwafin mutum (Abatar) bayan daukar murya da bidiyon mutum na sa’o’i ta yadda zai dauki yanayin motsin fuskar mutum da sauka da tashin muryarsu.
“Mukan samar da tamka ta surar mutum da kimanin kashi 96.,” in ji Michael Jung, shugaban sashen kudi na kamfanin DeepBrians AI.
Ya kara da cewa “Ta yadda iyalan mamaci ba za su ji wani iri ba idan suna tattaunawa da hoton nasa, duk kuwa da cewa ba na gaske ba ne.”
Kamfanin na da yakinin cewa wannan ci gaba ta fasaha za ta zamo wani bangare na abin da ya shafi mace-mace, “Inda za mu iya shiryawa kafin lokacin mutuwa, ta yadda za mu bar wani abu da za a ci gaba da tunawa da mu har abada.”
Tsarin yana da tsada, kuma ba kowa ne ke iya kirkirar kwafen dan uwansa ba, kamfanin ne ke yi.
Dangi kan biya kamfanin kudin da suka kai dalar Amurka 50,000 domin su aikin nadar bidiyon ‘yan’uwan nasu da kuma yin kwafen.
Duk da tsadar abin, wasu masu zuba jari na da yakinin cewa mutane za su karbi tsarin, har ma kamfanin na DeepBrain ya tara kudi dalar Amurka miliyan 44 a gidauniyar da ya kafa.
Sai dai wata kwararriya kan halayyar Dan’adam, Laberne Antrobus ta ce ya kamata a yi taka-tsantsan wajen amfani da irin wannan fasaha a lokacin da mutane ke cikin jimami.
“Rashin wani namu abu ne da ke girgiza mutum, ka da ya zama sai ka ni kamar ka kusa komawa daidai amma wani abu ya sake mayar da kai.
“Tunanin cewa za ka samu damar jin muryar wani naka da ya rasu ko kuma ka ji su suna magana lamari ne da zai iya sanya mutum cikin rudani.”
Antrobus ta kara da cewa ka da mutane su gaggauta rungumar wannan fasaha ta yin magana da kwafen dan’uwansu da suka mutu. “Dole ne ka zama mai karfin rai kafin ka gwada yin haka. A bi abubuwa a hankali.”