Wata gobara ta kone wani kauye mai suna Barebari da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Shehu Sule Udi ne ya sanar da haka lokacin da yake zanta wa da manema labarai.
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
- EFCC Ta Gurfanar Da Farfesa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N1.4bn
Ya ce, gobarar ta tashi tashi ne da safe, ta kuma kone gidaje masu yawa da runbunan da aka adana amfanin gona da dabbobi da kuma wasu kadarori masu yawa.
Udi ya ce, an taba yin irin wannan gobarar sheka biyu da ta wuce a wannan kauyen, wadda ta yi sanadiyyar konewar rabin kauyen.
Saboda haka, sai ya yi kira ga mutanen wannan yanki da su kara lura sosai wajen yin amfani da wuta, domin guje wa afkuwar irin wannan nan gaba.
Ya ce, yanzu haka karamar hukumar ta shirya gudummowar da za ta bayar ga al’ummar da wannan abu ya shafa, sannan kuma ya roki hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa da ta jiha da kuma sauran al’umma da su taimaka wa al’ummar da wannan abu ya shafa.
Mai magana da yawun jami’an tsaro na NSCDC na jihar Jigawa CSC Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar wannan lamari.
Shehu ya ce, gobarar ta kone gidaje hudu kuemus da dabbobi masu yawa da kuma wasu muhimman kayayyaki.
Ya ce, gobarar ba ta kone kowa ba, kuma an samu nasarar kashe ta tun kafin ta yi mummunar barna.
Wannan gobarar ta faru ne, bayan wata da aka yi a wannan yankin wadda ta yi sanadiyyar konewar wasu kauyuka guda uku a karamar hukumar Kiyawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp