Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, ya tsira daga wani hatsarin mota da ya afku da yammacin Lahadi a kan hanyar Daura zuwa Katsina, yayin da yake gudanar da aiki.
Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai. Ya ce gwamnan na cikin ƙoshin lafiya kuma bai samu munanan raunuka ba.
Sanarwar ta ce, “Muna farin cikin tabbatar da cewa gwamna yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana cikin yanayi mai kyau, ba tare da wani mummunar rauni ba.”
Mohammed ya ƙara da cewa, “Gwamna Radda yana cikin farin ciki, yana godewa Allah Madaukaki bisa kariya da ya samu, tare da gode wa al’ummar Katsina da masu fatan alheri bisa addu’o’i da damuwa da suka nuna.”
Majiyoyi da suka san da lamarin sun shaida wa Solacebase cewa an gaggauta kai gwamnan zuwa Asibitin Tarayya da ke Daura domin yin binciken lafiyarsa a matsayin matakin kariya. Sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin hatsarin ko yawan mutanen da suka tsinci kansu cikin lamarin. Gwamnan ya ci gaba da hutu a ƙarƙashin kulawar likitoci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp