Akalla gwamnoni 23 da ke kan karagar mulki a fadin jihohi 18 ne suka sauya jam’iyyun siyasar da aka zabe su zuwa wasu jam’iyyu tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a 1999.
Jihohin Sakkwato, Imo, da Abiya su ne kan gaba wajen sauya sheka da gwamnoni masu ci suka yi cikin shekaru 24 da suka gabata, kamar yadda LEADERSHIP ta gano.
- NLC Ta Yi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki
- ECOWAS Ta Shimfida Sabbin Ka’idoji Domin Janye Wa Nijar Takunkumi
Yayin da Sakkwato ta ke da gwamnoni uku, jihohin Abiya da Imo suna da gwamnoni biyu kowanensu.
Bincike ya nuna cewa 13 daga cikin wadannan gwamnonin da suka sauya sheka sun fito ne daga Arewa, 10 kuma sun fito ne daga Kudu.
Haka kuma mafi yawan gwamnonin da suka fice jam’iyyunsu sun faru ne a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sauya shekar gwamnonin ta faru ne a tsakanin jam’iyyun siyasa 10, wasu daga cikin jam’iyyun babu su a yanzu sakamakon maja da suka yi da wasu jam’iyyun.
Jam’iyyun dai sun hada da All Peoples Grand Alliance (APGA), Alliance for Democracy (AD), All Nigeria Peoples Party (ANPP), Progressive Peoples Alliance (PPA) da kuma All Progressives Congress (APC).
Sauran sun hada da Peoples Democratic Party (PDP), Democratic People’s Party (DPP), Action Congress (AC), Labour Party (LP) da Zenith Labour Party (ZLP).
LEADERSHIP ta ruwaito cewa akwai hanyoyi guda hudu da za a iya tsige gwamna mai ci daga mukaminsa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Hanyoyin kuwa su ne mutuwa, yin murabus, rashin iya aiki da tsigewa. Amma sauya shekar jam’iyyar siyasa ba ya daya daga cikin hanyoyin.
Sai dai wasu gwamnoni bakwai sun sauya sheka tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, gwamnoni biyar kuma suka sauya sheka tsakanin 1999 zuwa 2007.
Haka kuma, a shiyyar Arewa maso Yamma aka fi yawan masu sauya shekar.
A wannan shiyya gwamnoni takwas da ke kan mulki sun fice daga jam’iyyunsu tare da komawa wasu jam’iyyun, wanda su ne jihohin Sakkwato, Zamfara, Kano, Kebbi da Jigawa.
Kudu maso Gabas kuwa, shi ne yanki na biyu wanda gwamnoni biyar daga Abiya, Imo da Ebonyi suka fice daga jam’iyyunsu a lokacin da suke kan mulki.
Arewa maso Gabas ita ma ba a bar ta a baya ba, inda aka samu rahoton gwamnoni uku da suka sauya sheka a jihohin Bauchi da Adamawa.
A jihohin Kudu maso Kudu kuwa, akwai Ribas, Cross River da Edo, inda su ma aka samu sauyin sheka guda uku tun daga 1999.
An samu wasu sun sauyin sheka biyu a yankin Arewa ta Tsakiya (jihohin Benue da Kwara).
Kamar Arewa ta Tsakiya, sauyin sheka biyu ne kawai ya faru a shiyyar Kudu maso Yamma (jihohin Legas da Ondo).
Jihohin Kaduna da Katsina ne kadai a yankin Arewa maso Yamma da gwamnoninsu ba su fice daga jam’iyyun da aka zabe su ba har zuwa karshen wa’adin mulkinsu a cikin shekaru 22 da suka gabata.
Gaba daya Jihar Sakkwato ce ke kan gaba a jadawalin gwamnonin da suka fi sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa.
Gwamnonin uku na jihar daga 1999 zuwa 2023, Attahiru Bafarawa, Aliyu Wamakko da Aminu Tambuwal duk sun yi sauyin sheka.
Yayin da Bafarawa ya fice daga ANPP zuwa DPP; wanda ya gaje shi, Wamakko ya fice daga PDP zuwa APC, shi kuwa Tambuwal ya fice APC ya koma PDP.
Jihohin Abiya, Adamawa, Imo, Zamfara suna da sauyin sheka biyu kowacce.
A Abiya, Orji Kalu ya fice daga PDP zuwa PPA, yayin da wanda ya gaje shi, Theodore Orji ya fice daga PPA zuwa PDP.
A Jihar Adamawa Boni Haruna ya sauya sheka daga PDP zuwa AC, yayin da Murtala Nyako ya bar PDP zuwa APC.
A Imo kuwa, Ikedi Ohakim ya sauya sheka daga PPA zuwa PDP, yayin da Rochas Okorocha ya bar APGA zuwa APC.
A Zamfara kuwa, Mahmuda Shinkafi ne, ya fice daga ANPP zuwa PDP, yayin da Matawalle ya fice PDP zuwa APC.
Wani abun ban mamaki kuwa shi ne, Gwamnan Jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya sauya sheka sau biyu a lokacin da yake kan mulki.
Ya fara ficewa daga PDP zuwa APC a shekarar 2013, sannan ya koma PDP a watan Yulin 2018.
A yankin Arewa maso Gabas kuwa, ba a samu masu sauyin shekar siyasar ba a jihohin Borno, Yobe, Gombe da Taraba ba.
Babu wani gwamna a jihohin Filato, Nasarawa, Neja da Kogi da ya sauya sheka a yankin Arewa ta Tsakiya.
A yankin Kudu maso Yamma, ba a samu sauya sheka a tsakanin gwamnoninsu ba na jihohin Oyo da Ekiti da Ogun da kuma Osun.
Har ila yau, jihohin Bayelsa, Akwa Ibom da Delta ba su fuskanci sauyin shekar gwamnoni ba tsawon wannan lokaci.
Haka ma a jihohin Kudu maso Gabas na Anambra da Enugu.
Manyan lauyoyi, sun koka game da al’adar sauya sheka daga ‘yan siyasa.
Lauyoyin sun ce rashin akida ne ke sa bayan an an kada wa mutum kuri’un da suka ba shi nasara a jam’iyya sannan a bar ta ya koma wata jam’iyyar saboda son rai.
Wani babban lauyan Nijeriya, Mista Abdul Balogun, ya ce ‘yan siyasa a kasar sun dauki ‘yan Nijeriya abin hawa na tsawon lokaci.
“Abin takaici, ‘yan siyasa ko yaushe suna tsallake abin da suka shuka a baya”, in ji shi.
A cewarsa, a halin yanzu, Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tauye sauya sheka ne kadai a kan ‘yan majalisar dokoki ta jiha da ta kasa.
Ya ce: “Sashe na 68 (1) na kundin tsarin mulki ya ce, Dan Majalisar Dattawa ko na Majalisar Wakilai zai bar kujerarsa da aka zabe shi, idan ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa kafin karewar wa’adin da aka zabe shi’.
“Amma me muke da shi a yau; ‘yan majalisa na yin yadda suke so ba tare da wani sakamako ba. Wani lokaci, wasu daga cikin wadannan dokokin suna nan amma ba a aiwatar da su ba. Har ila yau, wani lokaci, idan wasu daga cikin wadannan aka kai kotu, suna zama abun bacin raj ne kawai. Muna bukatar kafa misali don zama darasi ga ‘yan siyasa.”
A nasa bangaren, Barista Joel Amanda ya ce doka ta yi kunnen uwar-shegu kan sauya shekar gwamnoni.
“A sani na game da abubuwan da ke faruwa a kasar nan dangane da sauya sheka, babu wani gwamna da ya rasa kujerarsa saboda sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa wata.
“Wannan bai dace da martabar kasar nan da kuma tsarin zaben mu ba. Daga 1999 har zuwa yau, ba ni da masaniyar cewa an kori ko tsige wani gwamna sakamakon sauya sheka da ya yi ba,” in ji shi.
Wani lauya mazaunin Legas, Barista Saudi Hammed, ya ce sauya sheka na nuna rashin akida da dabi’u na siyasa.
Ya ce ‘yan siyasa ba wai kawai ana zabar su ba ne saboda kwarewarsu da kuma ficen da suka yi ba ne, har ma da karfi da kuma kimar jam’iyyun siyasar da suka yi takara.
“A duk duniya, jam’iyyun siyasa a tsarin dimokuradiyya ana bambanta su da akidunsu da yanayin tsarinsu. Abin bakin ciki, a Nijeriya wani abu daban ake yi. A maimakon haka, babban abin jan hankali ga siyasa shi ne irin abin da ake samu a gwamnati. Da zarar wadancan bukatu ba su biya, sai batun sauya sheka ya zama zabi na gaba,” in ji shi.