Bayanai sun nuna cewa, hauhawar farashin kayan abinci Nijeriya ya ragu da kashi 22.97 cikin 100 a watan Mayun shekarar 2025 daga kashi 23.71 cikin 100, a watan Afirilun shekarar 2025.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce, ta bayyana hakan; inda ta ce, hauhawar farashin ya ragu matuka da kashi 1.53 cikin 100, a watan Mayu daga kashi 1.86 na watan Afirilun, wanda ta sanar da cewa; hakan ya kuma nuna cewa, an samu raguwar farashin kaya a daukacin tattalin arzikin kasar.
- Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
- Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa
A cewar hukumar, an samu raguwar tsadar farashin kayan abinci da farashin tufafi da kuma samun raguwar farashin da ake karba a bangaren kula da kiwon lafiyar Dan’adam.
Kazalika, hauhawar farashin kayan abinci a kasar; ya ragu da kashi 21.14 cikin 100, a watan Mayu daga kashi 21.16 cikin 100 a watan Afirilun shekarar 2025.
A cewar hukumar ta NBS, an samu wannan raguwar farashin kayan ne, bisa gwajin da hukumar ta yi.
Sai dai kuma, hukumar ta bayyana cewa; an dan samu tashin farashin kayan da kashi 2.19 cikin 100 a watan Mayu daga kashi 2.06 a cikin 100 a watan Afirilun na 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp