Rundunar ‘yansandan jihar Bauci ta samu nasarar kama wasu mutum hudu suna cire kudin wata marigayiya ta POS A Bauchi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Bauci SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Ya ce, ranar 06/09/2022, wani mutum mai suna Samira Jibrin,wanda yake matsayin dan’uwan Jibrin Adamu,da ke garin Zalanga, ta karamar hukumar Ganjuwa,wanda ke aiki a ma’aikatar ilimi ta jihar Bauci a sashin kudi ya rasu ranar 02/12/2021, sai ‘yarsa ta tafi domin neman hakkinsu a ma’aikatar kudi ta jihar Bauci, sai aka gaya mata cewa, tuni an tura kudin asusun marigayin kuma har ma an cire ta POS.”
Majiyarmu ta ce, bayan kai kuka ga ‘yansanda na A’ Dibisional da ke shalkwatar ‘yansanda, nan da nan suka fara bincike inda suka fara gano cewa Nasiru Samaila ma’aikaci a ma’aikatar kudi ta jihar Bauci,ya hada baki da wasu mutum uku wato, Auwal Jibrin da Tijjani Mohammad wajen kwashe wadannann kudi.”
Haka kuma Faruk Mohammad Nasiru dalibi mai neman sanin makamar aiki mai suna Abubakar Tatari da aka tura shi ma’aikatar kudi ya yi amfani da takardun bogi ya fitar da kudi naira dubu dari uku da talatin da biyu, mallakar marigayin.
Bincike ya nuna cewa, Nasiru Samaila, ya yi amfani da dadewar da ya yi a ma’aikatar wajen kwashe naira 212,000.00.
Majiyar ta ci gaba da shaida mana cewa dukkan wadanda ake zargin sun tabbatar da zargin da ake yi musu na aikata laifin.
Sai dai daya daga cikin wadanda ake zargin Auwal Jibril wanda kuma wanda shi ma yana daga cikin ma’aikaci a wannan ma’aikata, ya samu naira dubu dari a matsayin nasa Kason.
Shi kuma Tijjani Mohammed da Kafe da Faruk Mohammed dalibi mai koyon sanin makamar aiki wanda ya zo daga makarantar Abubakar Tatari Ali Polytechnic wanda shi ma yake a wannan ma’aikata, shi ma ya ci naira dubu ashirin.
Sannan an samu naira 320,000.00 daga hannun wadanda aka kaman.
A karshe, kwamishinan ‘yansanda ya umarci a kai wadanda ake zargin kotu.