A yayin da sace-sacen jama’a ke kara kamari a babban birnin tarayya Abuja, an kama wasu jami’an ‘yansanda bisa zargin kwatar naira miliyan 29.9 daga hannun wani mazaunin Abuja.
Lamarin, a cewar Harrison Gwamnishu, dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, ya faru ne a watan Janairu.
- An Cafke Wata Mata Bisa Laifin Safarar Yara 42
- Tsigaggen Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Liman Ya Sake Lashe Zaben Cike-gurbi
Gwamnishu, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo ta shafinsa na X (Twitter) cewa, jami’an ‘yansandan sun yi garkuwa da dan kasuwar ne a Abuja inda suka tsare shi har sai da ya mika musu dukkan kudaden da ke cikin asusun bankinsa. Daily Trust ta rahoto
Daga nan ne suka dage sai ya kira ‘yan’uwa da abokan arziki su ci gaba da tura masa kudi kafin a sako shi.
Da yake tsokaci kan wannan lamari a ranar Talata, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, yayin da yake tabbatar da kama wasu daga cikin masu laifin, ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike kan lamarin kuma za ta tabbatar da adalci.
“Muna kan binciken lamarin, kuma za a yi adalci, kamar yadda aka kama wasu da ake zargi.” kamar yadda ya rubuta.