• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Jariri Ke Koyon Tsotsar Nonon Uwa Kafin Haihuwa

by Sani Anwar and Sulaiman
1 month ago
Jariri

Babu shakka, Allah gwani ne cikin aikinsa da kuma mulkinsa. Yau za mu yi nazari a kan yadda Allah ya shirya jariri, domin sanin yadda zai iya tsotsar nonon mahaifiyarsa, ba tare da wani ya koya masa ba.

Bisa al’ada, tsotsar nonon uwa, aiki ne na musamman da yake bukatar a koya wa mutum, domin ya iya. Amma saboda Allah ya san ba zai yiwu a iya koya wa jariri wannan aiki na tsotsar nonon mahaifiyarsa ba, cikin rahamarsa da ikonsa; sai ya hutar da mu.

  • An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
  • Cire Tallafin Wutar Lantarki Zai Kara Kuntata Rayuwar ‘Yan Nijeriya – Kungiyar Kwadago

Tun jariri yana cikin uwa, tsakanin mako na 13 zuwa mako na 26, Ubangiji yake fara shirya jariri ta hanyar kimsa masa ilhamar tsotsar nonon mahaifiyarsa.

LABARAI MASU NASABA

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.

Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.

Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu ne shiryayye da Allah SWT.

Saboda haka, wannan ilhama ta tsotsar nono; tana daukewa a tsakanin watanni sha biyu (12), lokacin da ake shirye-shiryen yaye yaro daga shayarwa.

Har wa yau, bayan ilhamar tsotsa da ake kira a turance ‘Sucking refled’, akwai kuma wata ilhamar da ake kira da ‘Rooting refled’, ita kuma wannan ilhamar tana taimaka wa jarirai, su iya lalubo kan nonon mahaifiyarsu, ko da kuwa idonsu a rufe yake ko kuma a cikin duhu.

Bugu da kari, akwai kuma ilhamar hadiya, wato ‘Swallowing reflex’, bayan an tsotsi nonon; ana kuma bukatar a hadiye shi.

Don haka, ta kan wadannan ilhamomi guda uku ne da Ubangiji ya yi wa jarirai suke iya lalubo nonon mahaifiyarsu, sannan su tsotsa; har kuma su hadiye ba tare da wani mahaluki ya koya musu ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Kiwon Lafiya

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?
Kiwon Lafiya

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
Matsalar Tasgadewar Kashin Baya
Kiwon Lafiya

Matsalar Tasgadewar Kashin Baya

September 27, 2025
Next Post
Sin Da AU Sun Sabunta Hadin Gwiwa Game Da Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani Wajen Raya Noma A Afirka

Sin Da AU Sun Sabunta Hadin Gwiwa Game Da Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani Wajen Raya Noma A Afirka

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025
Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta

October 13, 2025
NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3

October 13, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.