Tun bayan daura auren mawaki Dauda Adamu Kahutu Rarara da amaryarsa jaruma kuma mawakiya Aisha Humaira ake ci gaba da tattaunawa kan bikin a kafofin sadarwa musamman bayan shagalin cin abincin dare na bikin da aka yi a Jihar Kano.
Daga cikin abubuwan da suka dauki hankali sun hada da adon da amarya da ango suka sha, kwalliyar da aka yi a zauren walima da kuma manyan bakin da suka halarci shagulgulan bikin a mabanbantan lokuta, biki ne da aka yi na kasaita musamman ganin yadda Rarara ke jan zarensa a wannan lokaci har ma wasu ke kwatanta shi da shahararrun mawakan kasar Hausa da suka shude, sanadiyyar baje-kolin basirar da yake yi a cikin wakokinsa.
- Wakilin Sin Ya Soki Yadda Amurka Ke Tafiyar Da Kudurin Takunkuman Sudan Ta Kudu
- Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB
A wani rahoto da BBC Hausa ta fitar mun tsakuro maku yadda jarumai da mawaka a masana’antar Kannywood suka auri junansu, dukkan wadannan aurarrakin anyisu cikin annashuwa da kaunar juna, akwai wadanda suke har yanzu a matsayin ma’aurata yayinda wasu kuma mai rabawa ta raba.
Dauda Adamu Rarara da Aisha Humaira
A ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2025 ce aka daura auren Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa Aisha Ahmad wadda aka fi sani da Aisha Humaira a birnin Maiduguri da ke Jihar Borno, an dade ana rade-radin akwai soyayya tsakanin ma’auratan biyu, amma a duk lokacin da aka tambaye su, sai su ce aiki da ne ya hadasu ba wani abu ba.
A shekarar da ta gabata Rarara ya rera wata waka mai taken ‘Aisha’, wadda a ciki ya baza kalaman soyayya har aka yi ta cewa da ita yake yi, amma sai aka yi amfani da wakar a fim din da ita jarumar ta shirya mai suna ‘A cikin biyu’ wanda Ali Nuhu ya hau a matsayin mijinta a wannan shirin.
Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai jiga-jigan yan siyasa irin su tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Barau Jibrin da sauransu.
Abubakar Bashir Maishadda da Hassana Muhammad
Daya daga cikin masu shirya fina-finai a masana’antar Kannywood Abubakar Bashir Maishadda wanda ake wa lakabi da ‘king of bod office’ saboda yadda yafi mayar da hankali wajen haska fina finansa a gidajen sinima.
Furodusan ya auri jaruma Hassana Muhammad, wadda ta fito a matsayin babbar jaruma a wasu fina-finan kamfaninsa, ciki har da shirin Hauwa Kulu da sauransu, an daura aurensu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris na shekarar 2022 a Masallacin Murtala da ke Kano.
Maishadda ya yi aure ne a lokacin da finafinansa suke tashe a masana’antar, inda yake fitar da fina-finai manya tare da jarumai mata da suke tashe a wannan lokacin, hakan ya sa aka rika alakanta shi da jarumai mata da yawa da suke fitowa a finafinansa.
Sani Danja da Mansurah Isah
Daya daga cikin auren yan Kannywood da ya kasance daya tamkar da goma kuma akayi bikin da za a dade ba a manta da shi ba shi ne na taurari biyu da suke tashe a lokacin da suka yi aure, wato Sani Musa Danja da Mansurah Isah, a ranar 14 ga watan Yuli na shekarar 2007 ne aka yi bikin auren jaruman, inda aka gudanar da biki na kece raini da kasaita.
Sani Danja ya yi tashe a shekarun baya hakazalika ya samu farin jini wurin ‘yanmata inda aka rika alakanta shi da taurari mata daban daban, daya daga ciki da ta yi fice ita ce Maryam Jan kunne, amma daga bisani ya rufe kunnensa ya zabi Mansurah Isah domin ta zama uwar ‘ya’yansa.
Sani Danja da Mansurah suna cikin yan fim na farko-farko da suka auri juna, kuma suka dade suna tare kafin auren ya mutu a shekarun baya, Allah ya albarkaci auren da yaya hudu mace daya Iman sai kuma maza uku da suka hada da Khalifa, Sultan sai kuma dan autansu Sudais.
Ummi Rahab da Lilin Baba
Wani auren da ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta shi ne na Ummi Rahab da angonta Lilin Baba, Ummi ta taso cikin masana’antar Kannywood a matsayin ta hannun damar babban tauraro Adam A. Zango, tun daga fim din da ta fara fitowa wato ‘Ummi’, a lokacin da Ummi ta nuna zata auri Lilin Baba an yi ta rade-radin cewa Adam Zango bai so hakan ba, sai dai duk da haka an daura auren kuma Ummi da Lilin Baba na ci gaba da zamansu a matsayin mata da miji.
Yayin da wasu ke zargin Ummi Rahab da juya wa wanda ya raine ta a masana’antar baya, wasu kuma sun zargi Zango da kokarin hana matashiyar rawar gaban hantsi, an daura auren Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar Asabar 18 ga watan Yulin shekarar 2022 a Tudun Murtala da ke Kano.
Fati Muhammad da Sani Mai Iska
Wadanda suka dade su na bibiyar harkokin fim din Hausa sun san irin tashen da Fati Muhammad ta yi, a matsayin daya daga cikin taurari mata na farko-farko da tauraruwarsu ta haska a shekarun baya a masana’antar Kannywood, wasu ma na ganin cewa ya zuwa wannan lokaci babu tauraruwar da ta shiga zukatan masu kallo kamar yadda Fati Muhammad ta yi a lokacin da take zamaninta.
Auren jarumar da Sani Mai Iska ya bai wa mutane da dama mamaki kasancewar an fi alakanta ta da wasu daban kamar Ali Nuhu duba da cewar sun yi zamani a tare inda suka fito a manyan fina finai da dama kamar Sangaya da Mujadala, aurenta da Sani Mai Iska ya ci gaba da jan hankali musamman ganin yadda suka bar kasar zuwa Birtaniya bayan auren domin cin amarci a can.
Ahmed S. Nuhu da Hafsat Shehu
Wani aure da ya dade a zukatan masoyan fina-finan Huasa shi ne wanda aka yi tsakanin jarumi Ahmed S Nuhu da abokiyar aikinsa Hafsat Shehu, masoyan biyu sun kasance abin so ga mutane da dama da ke kallon fina-finan Hausa na wancan lokacin, hakan bai rasa nasaba da shaidar da aka yi wa Ahmed na kasancewa mai son zaman lafiya da iya zama da mutane a ciki da wajen masana’antar.
A bangare daya Hafsat kan fito a yawancin fina-finai a matsayin mai sanyin zuciya da fara’a, lamarin da ya sa take burge masu kallo, tauraruwar ta fara tashe ne bayan fim dinta na Zabari ta kamfanin FKD ya shirya, sai dai auren bai dade ba, kasancewar Ahmed ya rasu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota da ya rutsa dashi a garin Azare na Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Shu’aibu Lawan Kumurci Da Balaraba Muhammad
Wani babban al’amari da ya faru a shekarun baya a masana’antar Kannywood shi ne aure tsakanin jarumi Shuaibu Lawan Kumurci da Balaraba Muhammad wanda a wancan lokacin ya zama daya daga cikin auratayya ta farko-farko da aka kulla a tsakanin jaruman masana’antar.
Duk cewa auren bai dade ba Allah ya dauki rayuwar Balaraba, amma dai auren ya kasance wanda aka dade ana mamakinsa a Kannywood duba da cewar ana yi wa Kumurci kallon irin mutanen nan masu zafi yayin fitowa a cikin fina-finai, ba kamar Balaraba wadda da dama ke gani a matsayin mace mai sanyin hali ba.
Wasila Isma’il da Al’amin Ciroma
Fim din Lerawa Production da ake kira Wasila, shi ne ya fito da Wasila Isma’il a duniyar fim din Hausa, aurenta da Al’amin Ciroma ya ja hankali sosai, duk da cewa a lokacin ba a samu yawaitar kafofin sada zumunta irin yanzu ba, auren ya dauki hankali ne saboda ya zo a daidai lokacin da masu kallon fina-finan Hausa suke ci gaba da tattaunawa game da fim din ‘Wasila’
Wasila Isma’il wadda ta fito a matsayin matar Ali Nuhu cikin fim É—in ‘Wasila’ bayan tafka soyayya mai ratsa zukata, ta jefa masu kallo cikin jimami bayan cin amanar Jamilu da wani tsohon abokinta mai suna Moda, soyayyar Wasila da Jamilu na daga cikin soyayya mafi zafi da aka taba gani a duniyar fina-finan Hausa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp